Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Mace Ta Farko a Matsayin Shugabar Jami'ar Gadau

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Mace Ta Farko a Matsayin Shugabar Jami'ar Gadau

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta naɗa sabuwar shugabar Jami'ar jihar watau Sa’adu Zungur University da ke Gadau
  • Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da tsohon kwamishinan Ilimi na jihar, Dakta, Aliyu Tilde, ya fitar ranar Litinin
  • Farfesa Fatima Tahir, mace ta farko da ta zama Farfesa a ƙaramar hukumar Bauchi, ita Allah ya ba wannan muƙami na VC

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya naɗa mace ta farko da ta zama Farfesa daga ƙaramar hukumar Bauchi, Farfesa Fatima Tahir, a matsayin sabuwa shugabar jami'ar jiha (VC).

Gwamnan ya amince da naɗin Farfesa Fatima Tahir a matsayin VC ta jami'ar jihar Bauchi (BASUG) wacce aka raɗa wa, Sa’adu Zungur University.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.
Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Mace Ta Farko a Matsayin Shugabar Jami'ar Gadau Hoto: leadership
Asali: UGC

Tsohon kwamishinan ilimi na jihar da ya sauka a makon da ya gabata, Dakta Aliyu Tilde, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Fara Ƙalaman Nuna Wanda Zai Mara Wa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa har zuwa yanzun gwamnatin Bauchi ba ta maye gurbin Tilde ba, wanda ya yi murabus daga muƙaminsa kwanaki kaɗan da suka shige.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba da jimawan nan ba gwamnatin Bauchi ta amince da naɗin Farfesa Fatima Tahir a matsayin sabuwar VC ta jami'ar Sa'adu Zungur da ke Gadau," inji Tilde.

Yace sabuwar shugaban jami'ar ta zo na ɗaya daga cikin jerin manema 12, waɗanda aka zakulo kana aka masu Intabiyu kan muƙamin a wata ɗaya da rabi da ya gabata.

Legit.ng Hausa ta gano cewa Fatima Tahir ta zama Farfesa mace a Microbiology kuma ta farko da jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta samar.

Haka zalika Farfesa Fatima ta yi aikin koyar wa a jami'ar ATBU kuma daga baya ta koyar a jami'ar BASUG kafin yanzun da aka naɗa ta VC a makarantar.

Kara karanta wannan

Dalilin da Ya Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Ɗaya Ba, Sanatan PDP Ya Faɗi Abinda Ya Hango

Bugu da ƙari Farfesar ta yi aiki a matsayin mataimakiyar VC watau (DVC) mai kula da bangaren koyarwa a jami'ar sojojin Najeriya dake Biu, jihar Borno a 'yan shekarun nan.

El-Rufai, Ganduje, da Gwamnoni 5 da ba za su Nemi Kujerar Sanata Bayan Barin Ofis ba

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin gwamnonin da wa'adinsu zai kare a 2023, waɗanda ba zasu nemi Sanata ba a zaɓen 2023

An saɓa ganin gwamnonin da idan wa'adin mulkinsu zango na biyu ya kare suna neman zarcewa majalisar dattawan Najeeiya.

Amma waɗannan da suka hada da gwamna Kaduna, Kano da sauransu ba zasu nemi yin ritaya a kujerar Sanata ba a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262