An Samu Wadanda Za Su Kai Bankin CBN Kotu a Kan Tsarin Cire N20, 000 a Rana

An Samu Wadanda Za Su Kai Bankin CBN Kotu a Kan Tsarin Cire N20, 000 a Rana

  • Femi Falana SAN ya fitar da jawabi yana cewa tsarin da CBN zai kawo a Junairun 2023 ya saba doka
  • Fitaccen Lauyan mai kare hakkin Bil Adama ya bukaci Muhammadu Buhari ya sa a soke tsarin nan
  • ‘Yan kungiyar masu POS sun shirya daukar hayar Falana ko wani Lauya domin suyi karar bankin CBN

Abuja - Babban Lauyan mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana ya soki sabon tsarin babban bankinkasa watau CBN na takaita cire kudi a Najeriya.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin, Femi Falana yace tsarin ya sabawa ka’ida, don haka ba za ta yiwu ya yi aiki ba, The Cable ta fitar da rahoto.

Lauyan yake cewa tsarin ya ci karo da sashe na 2 na dokar hana safarar kudi ta shekarar 2022, yace N5m ne abin da doka ta haramta yawo da shi.

Kara karanta wannan

A Dare Daya, CBN Ya Kawo Tsarin Da Mutane Miliyan 1.4 Za Su Rasa Aiki – Kungiya

Masanin shari’ar yace ba ayi wa wannan doka kwaskwarima ba, don haka babu yadda Gwaman CBN zai takaita cire kudi zuwa N100, 000 a mako.

Jama'a suyi watsi da tsarin - Falana SAN

Falana ya yi kira ga al’ummar Najeriya suyi watsi da wannan sanarwa da ya ce ta saba doka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto Lauyan yana kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin bankin CBN su janye wannan tsari da zai kawo kunci.

Gwamnan CBN
Shugaban Kasa da Gwamnan CBN Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Za a iya zuwa kotu da AMMBAN

A rahoton da muka samu a Punch, ta kai Falana yana cewa zai shigar da karar babban bankin idan ba a janye tsarin da ake shirin dabbakawa ba.

Shugaban kungiyar AMMBAN ta masu sana’ar POS, Victor Olojo ya shaidawa jaridar za su dauki hayar Femi Falana wajen shigar da kara a kotu kan batun.

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

Lauyan ‘Yan AMMBAN, Douglas Okojie ya kammala shirye-shiryen yadda za su je kotu da CBN ko da kuwa wani Lauyan dabam aka samu da Falana.

Daga 9 ga Junairun 2023, babu wani mutum da ya isa ya cire fiye da N20, 000 a rana ko N100, 000 a mako ba tare da ya bi wasu tsauraran matakai ba.

Za a rasa hanyar neman abinci?

An samu labari masu POS suna kukan suna bukatar fiye da wadannan kudi domin gudanar da kasuwancinsu, idan ba haka ba, za a haramta masu nema.

Masana tattalin sun ce tsarin zai jawo rashin ayyukan yi da karin wahalar kasuwanci musamman a karkara inda babu cigaban fasahohin zamani.

Amma CBN yayi karin haske cewa za ayi la’akari da sana’ar POS, za a iya janye masu kaidin. Ana sa ran wannan zai sa mutane ba za su rasa aikinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng