Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Babbban Birnin Jihar Ebonyi

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Babbban Birnin Jihar Ebonyi

  • Wasu 'yan bindiga sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi
  • Rahotannin da muka samu sun nuna cewa mutane sun gudu zuwa gidanjensu, wasu sun nemi ɓuya a wurare daban-daban
  • 'Yan ƙungiyar aware sun kafa dokar zaman gida ta kwana 5 daga ranar Jumu'a, lamarin da Jama'a basu yadda ba

Ebonyi - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun shiga Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi lamarin da ya sa mutane suka fara gudun neman tsira.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa lamarin ya jawo ihoce-ihoce da tashin hankali a birnin yayin da 'yan kasuwa suka garƙame shagunansu suka koma gida bisa tilas.

Harin yan bindiga a Ebonyi
Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Babbban Birnin Jihar Ebonyi Hoto: thenation
Asali: Twitter

Wasu mutane da dama sun ruga neman mafaka a Otal Otal da wasu wurare da suke ganin zia fi tsaro ko tsoron faɗawa hannun yan bindigan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Aka Tsinci Gawar Budurwa Cikin Wani Yanayi a Babban Birnin Jihar Arewa

Wani mutumi, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa saboda halin tsaro, yace shi kansa ya gudu zuwa wani Otal domin ya samu wurin ɓuya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na ɓoye a Otal yanzu haka, na fito sayen katin waya ne a gefen gidan gwamnati kawai sai na ga mutane na gudu. Cikin hanzari 'yan kasuwa suka maida kayayyakinsu cikin shago."
"Jami'an 'yan sanda dake aiki a kan Titin dake gefen gidan gwamnati ba su yi wata-wata ba suka sauya kayan jikinsu. Na fito daga mota saboda karar harbe-harbe a titin zuwa Kpirikpiri."

"Mutane sun maida kayansu cikin shago a kan tsohon Titin zuwa Enugu, idan kana gida karka hito har sai komai ya lafa," inji mutunin.

Bidiyoyi da Hotunan dake yawo a soshiyal midiya sun nuna yadda nutane ke guje-gujen neman tsira zuwa wurare daban-daban.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Sau 5 Ina Zama da Gwamna Wike, Atiku Abubakar Ya Fallasa Inda Matsalar Take

Wani mazauni yace bisa dole ya garzaya zuwa gidan abokinsa domin neman tsira bayan jin ƙarar harbe-harbe.

"Yanzu haka ina gidan abokina, Na ji karar harbin bindiga kuma mutane na ta kokarin guduwa. Na yi kokarin zuwa layin Agwu daga titin Convent," inji shi.

Ana tsammanin 'yan ƙungiyar aware ne suka kai wannan harin, waɗanda suka kafa dokar zaman gida ta kwana biyar daga ranar Jumu'an da ta shige, dokar da mutane suka yi watsi da ita.

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa 'Yan Kasuwa Wuta a Jihar Katsina

A wani labarin kuma Yan ta'adda sun yi ajalin wasu 'yan kasuwa huɗu a jihar Katsina, wani mutum ɗaya na kwance a Asibiti

Wasu 'yan kasuwa daga ƙauyen Zandam dake yankin ƙaramar hukumar Jibiya sun gamu da ajalinsu a hanyar zuwa kasuwa.

Hukumar yan sanda ta sanar da cewa 'yan ta'adda sun harbi yan kasuwa 5 a harin, huɗu suka mutu nan take yayin da ɗaya na kwance a Asibiti.

Kara karanta wannan

2023: Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Gana da Gwamnan Tsagin Wike, Bayanai Sun Fito

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262