'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa 'Yan Kasuwa Wuta a Jihar Katsina, An Rasa Rayuka

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa 'Yan Kasuwa Wuta a Jihar Katsina, An Rasa Rayuka

  • Wasu miyagun 'yan ta'adda sun kashe 'yan kasuwa aƙalla huɗu a yankin karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina
  • Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sanda yace mutum biyar maharan suka harba, ɗaya na kwance a Asibiti
  • Jibiya na ɗaya daga cikin kananan hukumomin Katsina da ayyukan ta'addanci ya shafa a jihar da shugaban kasa ya hito

Katsina - 'Yan ta'adda sun kashe 'yan kasuwa huɗu ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Jaridar Punch ta tattaro cewa 'yan kasuwan waɗanda suka fito daga ƙauyen Zandam, suna kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a kusa da hedkwatar ƙaramar hukumar lokacin da suka faɗa komar yan bindigan.

Harin yan ta'adda a Katsina.
'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa 'Yan Kasuwa Wuta a Jihar Katsina, An Rasa Rayuka Hoto: punchng
Asali: Twitter

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina, Sufuritanda Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin.

SP Isa ya bayyana cewa 'yan bindigan sun harbi masu zuwa kasuwa mutum biyar kuma nan take mutane huɗu daga ciki suka cika.

Kara karanta wannan

Dalilin da Ya Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Ɗaya Ba, Sanatan PDP Ya Faɗi Abinda Ya Hango

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, kakakin 'yan sandan yace:

"Eh hakane, yan ta'adda sun harbi 'yan kasuwa biyar, hudu daga ciki suka rasu nan take yayin da ragowar ɗayan ya samu raunuka kuma an garzaya da shi Asibiti a cikin birnin Katsina domin kulawa da shi."

Mazauna yankin sun bayyana cewa faruwar wannan lamarin ya jefa tsoro a zuƙatan 'yan kasuwa waɗanda suka riga suka isa kasuwar tun farko.

Ƙaramar hukumar Jibiya na ɗaya daga cikin yankunan da ayyukan ta'addancin 'yan fashin daji ya addaba a jihar Kastina, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Idan baku manta a baya, gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya yi kira da mahukunta su bar mutane su mallaki makamai domin kare kansu.

Lamarin dai ya haddasa cece-kuce da mahawara mai zafi tsakanin mutane a ciki da wajen jihar Katsina, jihar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya hito.

Kara karanta wannan

An kassara 'yan bindiga yayin da 'yan sanda suka dakile wani hari, suka kama mutum 9 a Arewa

Yan bindiga sun kashe hakimin Yankuzo

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Basarake Mai Martaba a Jihar Zamfara

Bayanai sun nuna cewa Hakimin Yankuzo na masarautar Tsafe, Alhaji Hamza Abdullahi Kogo, ya rigamu gidan gaskiya ranar Asabar.

A ce hakimin ya rasa rayuwarsa sakamakon raunukan harbi da ya samu lokacin da 'yan bindiga suka kai masa hari a hanyarsa ta komawa gida daga wurin taro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262