‘Yan Sanda Sun Damke Boka Kan Zargin Damfara da Mallakar Dalolin Bogi
- Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa sun cafke wani boka kan zargin damfara tare da mallakar dalolin bogi a Yenagoa
- Nnedim Ikechukwu ya samu kwastomomi biyu da suka je neman layar sa’ar neman kwangila kuma suka yi s‘ar samu
- Sun karbo kudin kwangilar wanda ya kai N1.15b inda suka kai masa ya tsarkake su amma ya canza musu da na bogi tare da tserewa
Bayelsa - Jami’an sashen yaki da damfara na rundunar ‘yan sandan Najeriya a birnin Yenagoa dake Bayelsa masu ofishi a Zone 16 sun damke wani mutum da zargin damfarar N1.150 biliyan.
‘Yan sandan suna zargin Nnedim Ikechukwu dake zama Fatakwal mai sana’ar bokanci da mallakar $1,290,000 na bogi, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Kamar yadda ‘yan sandan suka ce, yayin da sashen yaki da damfarar ke bincike kan zargin wani mai korafi na damfararsa N1.150 biliyan da Nolan yayi, an je caje gidansa dake yankin Omogwa kuma an gano $1,290,000 na Bogi dake boye a wasu madaidaitan akwatuna biyu.
Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne
’Yan Sanda sun yi martani
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya na zone 16, CSP Ikwo Kelvin Lafieghe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace rundunar ta kara kama wanda ake zargin da laifin babbar damfara tare da mallakar dalolin bogi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust a ranar Lahadi ta tattaro cewa wanda ake zargin wanda ke ikirarin kasancewa mai maganin gargajiya, wasu ‘yan kasuwa biyu sun tunkareshi da ya samar musu da laya wacce za ta sa wani ‘dan kasar waje ya basu kwangilar mai ta miliyoyin Naira.
Kamar yadda majiyar tace:
“Bokan ya bukaci kowanne daga cikinsu ya bashi N550,000 kuma sun biya N1.6 miliyan. Wanda ake zargin ya hada kayar ya basu kuma a watan Yulin 2022 sun samu kwangilar man ta N1.150b.”
Sun zargi cewa, lokacin da suka kawo masa kudin domin tsarkake su, ya canza musu da dalolin bogi sannan ya gudu da na gasken.
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku
‘Yan Sanda sun kama matashi kan zargin damfara a Adamawa
A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun kama matashi da katikan ATM 10 a Yola.
Ana zargin matashin da canza wa jama’a katikansu idan sun je cire kudi.
Asali: Legit.ng