Gombe: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Halaka Mutum 3 Tare da Kone Amfanin Gona
- Rayuka uku sun salwanta yayin da amfanin gona mai tarin yawa ya kone sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai yankunan Amtawalam da Pobawure
- Gwamna Inuwa na jihar tare da Kwamishinan ‘yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru tare da jaddada cewa za a tabbatar da inganta tsaro
- Kwamishinan ‘yan sandan yace miyagu ne kawai masu laifin amma ba ya da alaka da siyasa, don haka za a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi
Gombe - A kalla rayuka uku ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan farmakin da ‘yan bindiga suka kai yankunan Amtawalam da Pobawure dake karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe.
A yayin jawabi bayan duba yanayin barnar a ziyarar da Gwamna Muhammadu Inuwa na jihar ya kai a ranar Juma’a, an tafka asarar kayan abinci, jaridar Punch ta rahoto.
Gwamnan ya kwatanta miyagun da ‘yan bindiga kuma masu satar shanu inda ya jaddada cewa abinda suka yi na iya janyo tashin hankalin da gwamnatinsa ba zata lamunta ba.
Daily Nigerian ta rahoto cewa, kamar yadda Yahaya yace, farmakin zai iya haifar da tashin-tashina a jihohin Filato da Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun zo ganin yanayin barnar da rayukan da aka rasa bayan farmakin ‘yan bindiga da masu satar shanu a yankunan Amtawalam da Pobawure.
“Abin yana da taba zuciya matuka saboda yanayin wurinmu akwai zaman lafiya da kuma alamu na nuna cewa illar lamurran ‘yan bindigan Bauchi da Filato ne yake zuwa jiharmu.”
- Yahaya yace.
Ya bayyana cewa yayi umarnin kafa matsayar ‘yan sanda yayin da yake jaddada amfanin jama’a wurin taimakawa tsaro.
Ya kara da cewa:
“Na umarci a kafa matsayar ‘yan sanda da hukumomin da suka dace don su tabbatar da tsaro da doka a wannan wurin kuma da izinin Allah zamu sauka duk matakin da ya dace na bada kariya ga dukiyoyi da rayukan jama’ar Gombe.”
Ba farmakin siyasa bane, ta’addanci ne, Kwamishinan ‘yan sanda
A bangarensa, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Oqua Etim, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun lalata amfanin gona inda ya kara da cewa:
“Sun zo don su lalata amfanin gona kuma ba su sace komai ba. Muna kan lamarin shiyasa muka zo nan tare da ran shi ya dade. Bayan samun labarin ya bada umarnin mu kasance a nan don kiyaye doka da oda.”
Etim ya bayyana cewa a harin babu zancen siyasa inda ya jaddada cewa ta’addanci ne kawai kuma rundunarsa da sauran jami’an tsaro ba zasu sassauta ba.
Yace:
“Wannan bashi da hadi da siyasa. Don haka mu cire siyasa daga lamarin nan domin siyasa tana tafiya lafiya kalau. An halaka mutum uku da suka hada da tsoho mai shekaru 90 tare da wasu mutum 2.”
Asali: Legit.ng