NRC ta Sanar da Sauya Jadawalin Kaiwa da Kawowar Jiragen Kasan na Abj-Kd

NRC ta Sanar da Sauya Jadawalin Kaiwa da Kawowar Jiragen Kasan na Abj-Kd

  • Hukumar kula da sufurin jiragen kasa, NRC, ta sanar da sauya jadawalin Kaiwa da kawowar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna da na Kaduna zuwa Abuja
  • Kamar yadda Pascal Nnorli, Manajan kula da ayyukan jiragen kasan ya bayyana, an rage mintuna 30 na tashin wasu jiragen kasan
  • Jiragen kasan da ya shafa ya hada da na karfe 3:30 na Idu zuwa Rigasa da kuma na karfe 2:00 na rana na Rigasa zuwa Idu dake Abuja

Abuja - Hukumar sufurin jiragen kasa, NRC, ta sanar da gyara jadawalin kaiwa da kawowar jiragen kasa biyu daga Idu dake Abuja zuwa Rigasa ta Kaduna, jaridar The Nation ta rahoto.

Pascal Nnorli, manajan ayyukan da suka shafi jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna, ya sanarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Juma’a cewa wadannan gyare-gyaren an yi su ne domin tabbatar da jiragen suna isa inda suka nufa a kan lokaci.

Kara karanta wannan

An Samu Karin Talauci Duk Da Tallafin N3.5tn DaGwamnatin Tarayya Ta Bayar

Jirgin kasa
NRC ta Sanar da Sauya Jadawalin Kaiwa da Kawowar Jiragen Kasan na Abj-Kd. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yadda canjin ya kasance

Kamar yadda Nnorli yace, jiragen kasan zasu dinga tashi mintuna talatin kafin lokacin da suka saba tashi a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

“AK3 daga Idu a Abuja wanda ya saba tashi karfe 3:30 na dana ya isa Rigasa dake Kaduna karfe 5:38 na yamma yanzu zai dinga tashi da karfe 3:00 na yamma ya isa Kaduna karfe 5:08 na yamma.
“Hakazalika jirgin kasan KA4 na karfe 2 na yamma dake tashi daga Rigasa a Kaduna yanzu zai dinga barin Rigasa da karfe 1:30 na rana kuma ya isa Idu dake Abuja da karfe 3:37 na yamma a maimakon karfe 4:07 na yamma.”

Jaridar Punch ta rahoto cewa, kamar yadda manajan yace, gyaran zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Disamba.

Norli ya jaddada mayar da hankalin hukumar wurin tabbatar da kariyar fasinjoji da kadarorin dake hawa jiragen a kowanne lokaci.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: CBN ta Fitar Da Sabbin Matakai 5 Kan Hada-Hadar Kudi a Bankuna

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya bayyana cewa an dawo da karakainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 5 ga watan Disamba, sama da wata 8 bayan da aka dakatar da shi.

Jiragen kasan Abuja Kaduna sun dawo aiki bayan wata takwas

A wani labari na daban, Jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna sun dawo karakaina bayan kwashe watanni takwas basu aiki.

Sai dai bayanai sun nuna cewa babu fasinjoji masu yawa kamar yadda aka saba gani saboda tsoro da jama’a ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel