Budurwa Ta Fusata da Babbar Kawarta Kan Yadda Ta Ci Amanarta a Kan Saurayi

Budurwa Ta Fusata da Babbar Kawarta Kan Yadda Ta Ci Amanarta a Kan Saurayi

  • Wata kyakkayawar budurwa ta bayyana yadda kawarta ta ci amanarta bayan da ta bayyana mata sirrinta
  • Budurwar ta bayyana cewa, ya radawa kawarta abubuwan da ta shirya siyawa saurayinta a murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • Sai dai, kawar ta zaga budurwar, ta siyo kayayyakin kawai ta kaiwa saurayin ba tare da sanin budurwar tasa ba

Wata budurwa mai suna @humancentipeachh a shafin sada zumunta ta bayyana yadda kawarta ta yaudare ta duk kuwa da amintar da ke tsakaninsu.

Ta ce ta bayyanawa kawar ta cewa, bikin murnar zagayowar ranar haihuwar saurayinta ya zagayo, don haka gashi-gashi abin da ta shirya yi don ba shi mamaki.

Ta bayyanawa kawar dukkan sirrinta da abubuwan da za ta siya ma wannan saurayin nata, amma aka samu wani babban akasi na cin amana.

Kara karanta wannan

"Mun Rantse" Wata Budurwa Ta Kaiwa Saurayinta Da Ya Haukace Abinci, Bidiyon Yadda Ta Nuna Masa So Ya Ja Hankali

Budurwa ta fusata saboda kawarta ta yiwa saurayinta kyauta mai gwabi
Budurwa Ta Fusata da Babbar Kawarta Kan Yadda Ta Ba Saurayinta Kyautan Kayayyaki | Hoto: @humancentipeachh/TikTok
Asali: UGC

Kwatsam, kawai kawar ta siyo dukkan abubuwan da ta nufi siya, ta kaiwa saurayin a ranar bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta yada a TikTok cewa:

“Yayin da nunawa babbar kawata jerin kyaututtukan da na shirya siyawa saurayina a ranar bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa kawai sai ta siyo kayayyakin ta ba shi kyauta kafin na basi. Ina ta hutasshe ni, nagode?”

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a TikTok

Jim kadan bayan yada bidiyon labarinta, jama’a da dama sun bayyana kadan daga abubuwan da suke gani kan wannan lamari.

Mun tattaro muku kadan daga ciki kamar haka:

@chinfupas:

“Dukkanku masu yin martani kuna game da fata? Saurayinta ya samu kyautar da yake so ita kuwa kudinta sun huta.”

@hobizspringwater:

“Akalla dai kin samu kudin beli tun da ta siyo dukkan kayayyakin”

@megustatumadre69_:

“A ina kuke samo irin wadannan kawayen haka? Saboda na nisance su.”

Kara karanta wannan

Ta Turo Mun Hotuna: Matashi Ya Shiga Damuwa Yayin da Budurwarsa Ta Auri Wani Da Kudinsa

@yas2jjk:

“Wane irin saurayi kuke dashi haka? Ban gamu da saurayina ba tun da muka kammala karatu shekaru 4 da suka wuce.”

Matashi Ya Shiga Damuwa Yayin da Budurwarsa Ta Auri Wani Da Kudinsa

Matashi dan Najeriya ya shiga jimami da tashin hankali kan yadda wata budurwarsa ta yaudare shi ta auri wani ba shi ba.

A cewar rahoto, matashin ya shafe shekaru uku da budurwar suna cin soyayyarsu, sai kwatsam aka wayi gari ta bar hannunsa.

Matashin ya bayyana fushinsa da abin da ya faru, ya ce hakan bai cancanci ya faru da wani ba; mace ko namiji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel