Zakaran gwajin dafi: Ýan Najeriya sun ciri tuta a gasar musabaƙar Al-Qur’ani na Duniya

Zakaran gwajin dafi: Ýan Najeriya sun ciri tuta a gasar musabaƙar Al-Qur’ani na Duniya

- Yan Najeriya guda biyu sun taka rawar gani a gasar Al-Qur'ani ta Duniya

- Mahaddatan sun hada da Ustaza Faisal Muhammad Auwal da Ustaz Albashir Goni Usman

Wasu yan Najeriya su biyu matasa sun yi rawar gani, wanda ta cancanci yabo a gasar Al-Qur’ani na Duniya, inda suka wakilci kasa Najeriya, kamar yadda rahoton Rariya ya bayyana.

Mahaddatan Al-Qur’anin sun hada da Faisal Muhammad Auwal daga jihar Zamfara, da kuma Abashir Goni Usman wanda ya fito daga jihar Borno sun samu lambar yabo a karshen gasar Al’Qur’ani na duniya daya gudana a birnin Makkah, kasar Saudiyya, inji majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Uwargidar Gwamnan jihar Katsina ta raba ma mata 1,000 naira 5,000,000

Hafizi Faisal Muhammad, wanda ya wakilici Najeriya a matakin haddar Qur’ani , izifi 60 da kuma fassararsa ya fito ne daga jihar Zamafara, kuma shine mahaddacin da yazo na biyu a duniya gaba daya.

Zakaran gwajin dafi: Ýan Najeriya sun ciri tuta a gasar musabaƙar Al-Qur’ani na Duniya
Faisal da Goni

Sai kuma Albashir Goni mai shekaru 19, wanda ya wakilci Najeriya a matakin haddar Qur’ani izifi 60, inda shima ya samu nasarar zama na biyu, ya haddace Qur’ani yana mai shekaru 13, kuma ya halarci makarantar haddar Qur’ani ta Sheikh Idris Gone dake garin Maiduguri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng