Matashin Da Ya Rasa Mahaifiyarsa A Shekaru, Mahaifinsa a Shekaru 5 da Hannunsa a Shekaru 10 Ya Zama Lauya
- Wani matashi dan Najeriya ya yi fice a soshiyal midiya saboda labarinsa mai taba zuciya d a kuma yadda ya jajirce don ganin ya rabauta a duniya
- Inyene Dominic Akpan ya wallafa labarin yadda ya zama lauya bayan an rantsar da shi a matsayin cikakken lauya a ranar Talata, 6 ga watan Disamba
- Matashin ya bayyana cewa ya rasa iyayensa tun yana yaro karami sannan ya rasa hannunsa na dama amma duk da haka ya fuskanci rayuwa
Wani matashi dan Najeriya wanda ya zama lauya duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwa ya yi fice a Facebook.
Inyene Dominic Akpan ya wallafa labarin yadda ya yi fadi tashi a rayuwa bayan an rantsar da shi a matsayin cikakken lauya a ranar Talata, 6 ga watan Disamba.
Nan take labarin Inyene ya shahara domin sauran masu amfani da Facebook na ta wallafa labarin domin taya shi murna.
Inyene ya zama maraya tun yana karami
A cewar Inyene, ya rasa mahaifiyarsa yana shekaru hudu a duniya, mahaifinsa yana shekaru biyar da kuma hannunsa na dama yana shekaru 10.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk wadannan kalubalen na rayuwa basu hana Inyene kokarin ganin mafarkinsa ya zama gaskiya ba domin ya dai sai da ya yi karatun lauya kuma ya kammala.
Kalamansa:
"Daga rasa mahaifiyata a shekaru 4, mahaifina a shekaru 5 da kuma hannuna na dama a shekaru 10 zuwa zama Barista na farko kuma lauyan kotun koli na Najeriya a ahlina. Allah ne ya yi mun, tare da dangi da abokai kuma wata rana nan kusa ina fatan bayar da labarina."
Jama'a sun yi martani
Aniebiet Buka ta ce:
"Ina tayaka murna dan uwana na kaina, Allah ya albarkace ka."
Nyakno Asuquote ya ce:
"Ina tayaka murka abokina na kwarai. Rayuwarka izina ce. Asuquote na tayaka murna."
Bidiyon jinjira yar kwana daya da ta yi murtuk da fuska ya ja hankali
A wani labari na daban, wata jinjira sabuwar haihuwa ta haddasa cece-kuce a shoshiyal midiya bayan ta murtuke fuskarta murtuk kamar wata babba.
Mutane da suka yi martani sun ce sam alamu sun nuna bata shirya ma gwawarmayar duniya ba amma mahaifiyarta ta sullubo ta.
Asali: Legit.ng