Buhari da Shugabannin Afirka 48 da Za Su Halarci Taron Shugabannin Amurka da Afirka

Buhari da Shugabannin Afirka 48 da Za Su Halarci Taron Shugabannin Amurka da Afirka

  • Kasar Amurka ta gayyaci shugabannin nahiyar Afrika, shugaban kasa Muhammadu Buhari na daya daga cikinsu
  • Za a yi wani taron tattaunawa da shugabannin Afrika da na Amurka, ana sa ran halartar jiga-jigan duniya
  • Shugaba Buhari ya samu lambar karramawa daga gwamnatin kasar Guinea Bissau a cikin makon nan

FCT, Abuja - Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gayyaci shugabannin kasashen Afrika 49 da kuma shugaban kungiyar hadin kan Afrika zuwa wani taron shugabannin Amurka da Afrika da za a gudanar.

Za a yi wannan gagarumin taron ne a ranakun 13 zuwa 15 ga watan Disamban 2022 a birnin Washington DC, babban birnin kasar Amurka.

Wannan batu na gayyata dai ya iso Najeriya, kuma majiya tace ta samu bayanin ne a ranar Alhamis daga cikin wata sanarwa da aka fitar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Bayyana Asarar Naira Tiriliyan 10 da ke Jiran Najeriya a 2023

An gayyaci Buhari ya halarci wani taro a Amurka
Buhari da Shugabannin Afirka 48 da Za Su Halarci Taron Shugabannin Amurka da Afirka | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar, Biden ya yi imani da cewa, hadin kan Amurka da shugabannin Afrika, kungiyoyin farar hula, ‘yan kasuwa, mata da matasa abu ne mai muhimmanci wajen dakile kalubale masu yawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Manufar yin wannan taro mai dimbin tarihi

Manufar wannan taro mai dimbin tarihi dai ba komai bane face habaka siyasa, tattalin arziki, dabarun hadin kai gami da tattaunawar jama’a kan manufa iri daya don ci gaban Afrika.

Hakazalika, taron zai mai da hankali ga tattauna hanyoyin samar da abinci, inganta lafiya, yanayi da dai sauran abubuwan da ke shafar kasashen duniya, Economic Confidential ta ruwaito.

A cewar jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard, taron da za a yi zai ba da damar habaka dankon zumuncin Najeriya da Amurka tare da samar da damammaki ga kasashen.

A bangare guda, taron zai taimakawa Amurka da Amurkawa wajen jaddada zamantakewa da samun damar yin mu’amala da jama’ar Afrika.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Da Gaske Aminu Ya Gana Da Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Daga nan ta bayyana fatan shugaban kasa Muhammadu zai halarta tare da ba da gudunmawarsa da ma sauran ‘yan kasa da abin ya shafa.

Kasar Guinea Bissau Ta Karrama Buhari da Babbar Karramawar Kasa

A wani labarin kuma, an gayyaci Buhari zuwa kasar Guinea Bissau, inda aka ba shi lambar yabo da karrmawa mai girma na kasar.

Hakazalila, an kaddamar da wani titi da aka sanyawa sunan Buhari, karo na biyu kenan inda aka yi irin haka a Nijar.

Kasashen Afrika na yawan mutunta shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.