Tawagar Gwamna Ta Gwabza Hatsari, Direba Ya Mutu, wasu Sun Jigata
- Tawagar Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ta tafka hatsari inda daya daga cikin direbobi ya rasa ransa yayin da wasu suka matukar jigata
- Motar da Ramon Mustapha ke tukawa ta tintsira babu adadi inda tayi wurgi da shi kafin ta daidaita a titi, duk da bai saka damarar tuki ba
- Wata majiya da ta kasance ganau ta sanar da cewa an yi jana’izarsa a Amuloko dake garin Ibadan a jihar Oyo kamar yadda addinin Islama ya tanadar a ranar Laraba
Oyo - Wani direba dake tuka daya daga cikin motocin tawagar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya rasa ransa sakamakon hatsarin da ya tafka ranar Talata.
Mutum uku daga cikin tawagar sun rasa ransu yayin da Gwamna yake komawa Ibadan daga Saki inda yaje wani taro da mambobin jam’iyyar PDP.
An tattaro cewa, direban mai suna Ramon Mustapha ya rasa ransa a take saboda muguwar faduwar da yayi yayin da abun hawan da yake kai ya dawo ya tsaya bayan tintsirawa da yayi sau babu adadi.
Wata majiya tace da ace direban ya saka damarar tuki, da hakan bata faru ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata majiya wacce take cikin tawagar amma ta bukaci a boye sunanta tace direban ya buga kansa ne a yayin hatsarin.
An gano cewa motar da tayi hatsarin mai lambar ‘Zebra 4’ tayi watsi da wasu buhunan shinkafa wadanda wasu a cikin tawagar suka siyo.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa, an birne gawar marigayin direban a gidansa dake Amuloko, Ibadan kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Kiran waya da sakon kar ta kwana da aka dinga aikawa sakataren yada labaran gwamnan, Taiwo Adisa domin tabbatar da faruwar lamarin duk ba a amsa su ba.
Tawagar Yahaya Bello ta tafka hatsari
A wani labari na daban, Hukumar FRSC ta sanar da cewa wasu motoci cikin tawagar gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi sun tafka mugun hastsari a hanyar Abuja a ranar Litinin.
Kwamanda yanki na babban birnin tarayya Abuja, Mr Wobin Gora, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Abuja.
Gora ya sanar da cewa bai gama samun cikaken bayanin hatsarin ba amma ya tabbatar gwamnan baya cikin tawagar da lokacin da hatsarin ya afku.
Asali: Legit.ng