Tawagar gwamnan APC tayi hatsari a hanyar zuwa Abuja
Hukumar Kiyaye Hadura na kas FRSC ta ce wasu motocci cikin tawagar gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi sun yi mummunan hastsari a hanyar Abuja a yau Litinin.
Secta Kwamanda na babban birnin tarayya Abuja, Mr Wobin Gora, ne ya tabbatarwa Tribune Online afkuwar lamarin a Abuja.
Gora ya ce bai gama samun cikaken bayanin hatsarin ba amma ya tabbatar da cewa gwamnan baya cikin tawagar da lokacin da hatsarin ya afku.

Asali: UGC
Wani shaidan ido, ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa hatsarin ya afku ne saboda gudun fitan hankali da direbobin motoccin da ke ayarin gwamnan ke yi.
DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa (Bidiyo)
A wata rahoton, Legit.ng ta gwamna jihar Kogi, Yahaya Bello tare da tawagarsa suna daya daga cikin wanda suka kwashe suka gamu da masu zanga-zanga da suka rufe titin Abuja zuwa Lokoja a hanyarsa ta zuwa Abuja domin ganawa da shugaba Buhari.
A cewar, Akinti Onyegbule, sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kogi, direbobin tankan sun fara zanga-zangan ne bayan wani soja ya harbi tayoyin wata tanka.
Ya ce gwamnan ya kwashe kusan sa'a guda yana sulhu tsakanin direbobin da soji kafin masu zanga-zangan suka hakura suka janye motocinsu daga titin
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng