Babban Abin Bakin Ciki, Hawaye Yayin Da Babban Malamin Addini Ya Rasu A Najeriya
- Rabaran Dr Daniel Otoh, fasto a daya daga cikin shahararrun cocin Najeriya, The Shepherd's House Assembly, ya rasu
- Fasto Otoh, wanda kwararren likita ne, ya rasu a ranar Lahadi 4 ga watan Disamba, a cewar sanarwar da cocin ta fitar
- Yan Najeriya da dama sun yi alhihin rasuwar faston a yayin da cocin ta ce za a fitar da bayanai dangane da jana'izarsa
Cocin The Shepherds House Assembly, fitaccen coci a Najeriya, ta sanar da rasuwar fastonta, Rabaran Dr Daniel Otoh.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Fasto Mrs Jackie Talena a madadin cocin ya nuna cewa Dr Otoh, kwararren likita, ya rasu a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani sashi daga cikin sanarwar ta ce:
"Cike da kaduwa da bakin ciki amma da tawakalli a kalamansa, mu a cocin The Shepherd's House Assembly na sanar da rasuwar faston mu da muke kauna, miji, mahaifi kuma kwararren likita Rev. Dr. Daniel Otoh."
Cocin ta kara da cewa nan gaba za fitar da sanarwar ranar jana'izarsa idan an kamalla shirye-shirye.
Yan Najeriya sun yi alhinin rasuwar Rev. Dr Daniel Otoh
Lizzy Paul a Facebook ta ce:
"Allah ya jikan ran mammacin yasa ya huta, ina mika ta'aziyya ga iyalan Shepherd."
Evang Barnabas Tochukwu ya ce:
"Ta'aziyya ta ga iyalansa. Allah ya basu hakurin jure rashinsa."
Victor Terah-Patrick ya ce:
"Allah ya jikan ran dan uwanmu & Fasto, Dr Dan Otoh Allah ya gafarta maka. Allah ya bawa iyalansa hakuri & dukkan yan cocin Shepherd's House Assembly a duk fadin duniya. Tabbas mu baki ne a wannan duniyan. Sai mun hadu Fasto Dan."
Asiri Ya Tonu: Yan Bindigan Da Suka Shiga Gidan Sanatan APC Sun Fara Magana, Sun Faɗi Sunan Wanda Ya Tura Su
Babban sarki mai shekaru fiye da 100 a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
A wani rahoton daban, Onijagbo na Ijagbo a karamar hukumar Oyun a jihar Kwara, Oba Salawudeen Fagbemi Obembe II ya rasu.
Oba Fagbemi ya rasu ne a ranar 5 ga watan Disamban 2022 yana mai shekaru 110 a duniya kamar yadda Leadership ta rahoto.
Mai girma gwamnan jihar Kwara, Mr AbdulRahman AbdulRazaq, ya mika sakon ta'aziyya ga al'ummar masarautar Ijagbo kan rasuwar Oba Fagbemi.
Asali: Legit.ng