Fusatattun Matasa Sun Fatattaki Yan PDP Yayin Kamfen a Delta, Sun Nemi Su Yi Rantsuwa
- Ga dukkan alamu zaben 2023 zai banbanta da wadanda aka saba domin dai matasa sun farka daga bacci
- Matasa a jihar Delta sun fito fili sun fadama masu neman takara cewa ba za su zabi wadanda basa aiki daga tushe ba
- Matasa a garin Oko fatattaki shugaban marasa rinjaye a majalisad wakilai, Ndudi Elumelu inda suka hana shi kamfen a yankin
Delta - Shirin PDP na bin guduma-guduma don yin kamfen ya hadu da cikas a yankin Delta ta arewa yayin da fusatattun matasa a garin Oko suka hana su katabus a yankin.
Matasan sun hana yakin neman zaben ne saboda a cewarsu yan siyasa alkawaran karya suke daukarwa jama'a, jaridar Punch ta rahoto.
Musamman matasan suka hana shugaban marasa rinjaye a majisar wakilai, Ndudi Elumelu shiga garin kan gazawarsa wajen magance matsalolin da garin ke fuskanta a matsayinsa na dan majalisa tsawon shekaru.
Dalilin fushin matasan
Sai da dan takarar sanata, Ned Nwoko ya shafe tsawon awanni kafin ya lallashi matasan suka sauko suka saurare shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matasan wadanda suka saurari Nwoko sun koka kan mawuyacin halin da garin ya shiga tsawon shekaru.
Da yake jawabi a madadin kungiyar, shugaban matasan ya ce al'ummar garin sun gaji da alkawaran karya da yan siyasa ke yi masu.
Ya ce:
"Tun 1999, PDP ke zuwa nan don yakin neman zabe amma bayan zabe basa taba tunawa da garin Oko. Babu hanya, babu wuta da sauran ababen more rayuwa.
"Mun dade muna zaban wannan jam'iyya ta PDP a dum zabe amma babu abun nunawa. Elumwku ya dade yana zuwa da daukar mana alkawaran karya.
"Kuma zai sake zuwa don ya yaudaremu a karo na hudu, wannan shine fushinmu kuma bama son a sake mana irin wadannan alkawaran."
Matasan sun gabatar da bukatarsu
Sai dai kuma, matasan sun bukaci Elumelu da sauransu su je dakin tsafi na garin don daukar rantsuwa cewa za su magance matsalolin garin musamman hanyoyi idan aka zabe su.
A halin da ake ciki, Nwoko ya ba mutanen garin tabbacin cewa za a gina dukkanin hanyoyi daga Oko zuwa Ndokwa ta gabas.
Nwoko ya kuma yi alkawarin magance matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar garin duk shekara.
2023: Peter Obi ya ci zabe ya gama, Babachir Lawal
A wani labari na daban, Jigon jam'iyyar APC, Babachir Lawal ya bayyana cewa waji ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya lashe zabe a 2023.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce idan har Obi bai lashe zabe ba za su koma kasar Kamaru da zama saboda kunya.
Asali: Legit.ng