'Yan Sanda Sun Ceto Mutum Uku da Aka Yi Garkuwa da Su a Abuja, Sun Kwato Makamai
- Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ceto wasu mutane uku da 'yan bindiga suka sace a jiya Talata
- Rahoto ya ce, 'yan bindiga sun kai mummunan farko a Abuja, sun hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama
- Ba wannan ne karon farko da aka taba kai hari Abuja ba, kwanakin baya an kai hari har cikin wata babbar magarkama a birnin
FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun yi nasarar ceto mutum uku da aka sace a daren jiya Talata 6 ga watan Disamba yayin da ‘yan bindiga suka kai wani farmaki a wani yankin Kubwa.
Hakazalika, rundunar ta ce ta fara bincike don ganowa da dakile faruwar lamari irin wannan a babban birnin na tarayya.
Kwamishinan ‘yan sanda, Sunday Babaji ya bayyana cewa, gaggauta daukar mataki daga jami’an rundunar ne ya kai ga ceto mutum uku tare da kwato makamai, ciki har da bindiga kirar AK47 da dai sauransu.
Kakakin rundunar, Josephine Adeh ta tabbatar wannan ci gaban ne a ranar Laraba da safe, inji rahoton jaridar BluePrint.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An kai mummunan farmaki a Kubwa, an sace mutane, an harbe mutum biyu
Adeh ta bayyana cewa, binciken farko da hukumar ta gabatar ya nuna cewa, da misalin karfe 7:30 a dare ne wasu ‘yan bindiga suka farmaki yankin Kubwa, inda suka hallaka mutum biyu; Oshodi da Abdulwahab.
A cewar Adeh:
“Wadanda ake zargin sun tsere da mutane hudu yayin da suke barin wurin watakila saboda su kaucewa kamun ‘yan sandan da suka tunkare su yayin da aka tura jami’ai.”
Rahoto a baya ya bayyana cewa, an sace wata ‘yar bautar kasa da wasu mutum bakwai a daren ranar Talata, yayin da aka harbe wasu kuma har lahira, wasu kuwa suka samu raunukan harbin bindiga.
Biyu daga cikin wadanda aka sacen sun tsere daga hannuna ‘yan ta'addan da suka kai su kan dutse, rahotkn Vanguard.
Matakin da 'yan sanda ke dauka a yanzu
A halin da ake ciki, kwamishinan ya yi kira da kowa ya kwantar da hankali tare da natsuwa, domin an tura jami’ai kuma suna ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a yankin.
Ya kuma tabbatarwa jama’a cewa, bincike zai kai ga gano masu hannu a harin tare da kamo su a gurfanar dasu a gaban kotu.
Daga karshe ya bukaci jama’a da su ba da rahoton motsin ‘yan ta’addan ta hanyar kiran wadannan lambobin waya kamar haka: 08032003913, 08061581938, 07057337653, and 08028940883 ko kuma ta lambar mika koke: 0902 222 2352.
A jiyan ne wani rahoto yace an kuma kai hari a Wuse Zone 2, inda aka hallaka mutum daya tare da jikkata mutum biyu.
Asali: Legit.ng