Ku Taya Mu Tsare Kayayyakin Mu, INEC Ta Roƙi Yan Najeriya

Ku Taya Mu Tsare Kayayyakin Mu, INEC Ta Roƙi Yan Najeriya

  • Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta roki yan Najeriya su taimaka wurin kare kayayyakin hukumar
  • Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben na kasa ne ya yi wannan rokon yana mai cewa kayan INEC tamkar dukiyar kasa ne
  • Yakubu ya ce nauyi ne kan kowanne dan kasa ya bada gudunmawa wurin kare dukiyar kasa yayin da ya ke bada tabbacin yin zabe kamar yadda aka tsara

Abuja - Biyo bayan haren-haren da ake kai wa ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, jiya hukumar ta yi kira ga yan Najeriya su rika kallon kayayakinta a matsayin kayan kasa kuma su rika kare su gabanin babban zaben 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan rokon a taronsa da Kungiyar Dattawan Arewa Na Afirka ta Yamma da aka yi a hedkwatan INEC da ke Abuja, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari Ya Yi Kakkausan Gargadi Ga Sojoji, Ya Basu Muhimmin Aiki 1

INEC Office
Ku Taya Mu Tsare Kayayyakin Mu, INEC Ta Roƙi Yan Najeriya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma da tsohon mataimakin shugaban kasar Gambia, Fatoumata Jallow-Tambajang suka jagoranci tawagar.

Hakki ne kan dukkan yan kasa su kare kayayyakin kasa - Yakubu

Wani sashi na jawabin Yakubu:

"Akwai wasu bangarori kadan da ke bamu damuwa, wanda ya fi damun shine barazanar rashin tsaro a kasar. A kasa da mako biyu, an kai wa ofisoshin mu na kananan hukumomi uku hari, ya kawo jimmilar harin da aka zuwa bakwai a watan da ta gabata.
"Yayin da muke tabbatarwa yan Najeriya cewa za mu farfado daga hare-haren, kuma a yi zabe kamar yadda aka shirya, muna kira ga yan kasa su rika ganin kayan hukumar tamkar kayan kasa.
"Aikin mu ne baki daya mu hada hannu mu tsare su. Dole a dakatar da hare-haren a kuma kamo maharan tare da hukunta su cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

Na Shirye Kazancewa a Siyasar 2023, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Sahun Gaba Ya Fusata

Tunda farko, Koroma, ya ce sun taho Najeriya ne don yin sasanci kafin zabe don tattauna kan batutuwan da suka shafin nasarar zaben Najeriya da yankin, rahoton 21st Chronicle.

Jami'an Tsaro Sun Gano Wadanda Suka Cinna Wuta A Ofishin INEC

Yan sanda sun kama wasu da ake zargin yan haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa Biafra, IPOB, kan zargin hannu a kona ofishin INEC a jihar Imo.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, Mike Abattam ne ya sanar da hakan a Owerri, babban birnin jihar Imo yana mai cewa suna jefa bama-bamai a cikin ofishin INEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel