Daf da Buhari Zai Bar Mulki, Gwamnati Ta Kai Muhimmin Aiki Zuwa Garin Daura

Daf da Buhari Zai Bar Mulki, Gwamnati Ta Kai Muhimmin Aiki Zuwa Garin Daura

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ware N500m domin gina gwamnatin asibitin tarayya a garin Daura
  • Maganar da ake yi akwai irin wannan asibiti a Katsina, babu wata Jiha da take da asibitin har biyu
  • Akwai jihohi 15 da suke neman asibitin, amma gwamnatin tarayyar tana shirin sake gina wani a Katsina

Katsina - Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ware N500m a kasafin kudin 2023 domin a gina babban asibitin tarayya a garin Daura, jihar Katsina.

Premium Times ta rahoto cewa kundin kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaban kasa ya gabatarwa ‘yan majalisa ya nuna akwai kwangilar.

A cikin N20.5tr da Najeriya take sa ran kashewa a shekarar badi, N500m za su tafi ne wajen aikin gina cibiyar kula da lafiya a mahaifar shugaban kasa.

Idan aikin ya kammala, Katsina za ta zama jihar farko a Najeriya da ta mallaki cibiyoyin lafiya biyu.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

Katsina ta zarce sa'a

Yanzu haka akwai irin wannan katafaren asibiti a Katsina, a Najeriya ana da 22. Tazarar da ke tsakanin Katsina zuwa Daura ba ta kai kilomita 100 ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A lokacin da za a gina wani sabon asibitin a Daura – inda aka haifi shugaban Muhammadu Buhari, akwai jihohin da sam ba su da irin wannan asibiti.

Buhari
Shugaban Najeriya Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A yankin Kudu maso yamma, akwai makamancin asibitin a Ogun, Lagos, Ekiti da Ondo. A Kudu maso Kudu kuwa akwai su ne a Delta da Bayelsa kurum.

Kamar Neja-Delta akwai asibitocin a Imo da Abia a Kudu maso gabas. A Arewa maso gabas akwai su a Bauchi, Gombe, Taraba, Yobe sannan jihar Adamawa.

Neja, Kogi, Benuwai da birnin tarayya Abuja sun mallaki asibitin a Arewa maso tsakiya. Sai kuma Kebbi, Jigawa, Zamfara da Katsina suna da daya yanzu.

Kara karanta wannan

Kudin Da Ministan Jinkai Da Walwala Jama'a Tace An Mata Cushensu An Gano Na Menene

Babu FMC a Jihohi 15

Jihohin da suka rasa asibitin sun hada da Oyo da Osun sai Akwa-Ibom, Ribas, Edo da Kuros Ribas.

Haka zalika babu asibitocin tarayyar a jihohin Anambra, Ebonyi da Enugu, sai Kano, Kaduna da Sokoto, sannan babu a Filato da Kwara sai kuma jihar Borno.

Obasanjo yana neman bashi

Rahoton da aka fitar dazu ya nuna shekara uku da barin kujerar Shugaban Kasa, sai da Olusegun Obasanjo ya koma neman bashi daga abokan aikinsa a soja.

Da ya shiga matsayin rayuwa a mulkin Shehu Shagari, Obasanjo ya aika wasika zuwa ga Samuel Ogbemudia domin aron N80, 000, ya kula da gonarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng