Yadda Shugaba Buhari Ya Yi Kwanaki fiye da 200 a Asibiti, Ya Ziyarci Kasashe 40
- Babu mamaki Mai girma Muhammadu Buhari yana cikin shugabannin da suka fi yawo a Duniya
- Shugaban Najeriyan ya ziyarci kasashe sama da 40 daga lokacin da ya hau mulki a 2015 zuwa yau
- Buhari ya kuma shafe kwana da kwanaki a kasar asibitin Landan domin ya kula da lafiyar jikinsa
Abuja - Daga lokacin da Muhammadu Buhari ya karbi ragamar shugabancin Najeriya zuwa yau, ya shafe kwanaki akalla 225 bai ofis, yana asibiti.
Wani dogon rahoto da aka samu a jaridar Punch ya nuna a Fubrairun 2016 ne Mai girma Muhammadu Buhari ya tafi ganin Likitansa a karon farko.
Ziyarar farko da ya yi zuwa asibiti a Landan ya dauki kwanaki shida ne kurum. Bayan watanni hudu sai ya sake kwana goma ana duba kunnensa.
A ranar 19 ga watan Junairun 2017, shugaban kasar ya sanar da majalisa zai je Landan domin ya yi kwanaki 10, bai iya dawowa ba sai a Maris.
An yi kwana 100 Osinbajo yana rike da kasa
Jim kadan bayan dawowarsa Najeriya, Buhari ya sake tafiya Landan inda ya yi tafiyar da ta fi kowace tsawo, a lokacin ya shafe kwanaki 104 a Ingila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken da jaridar tayi, ya nuna shugaban kasar bai sake zuwa asibiti ba sai a watan Mayun 2018, a lokacin kwanaki hudu kurum ya dauka ana duba shi.
A watan Maris na shekarar 2021, kamar yadda ya saba, Buhari ya je Landan domin a duba lafiyarsa, bai wuce kwanaki 15 a can ba, sai ga shi ya dawo gida.
Bayan shekara daya, a watan Maris na shekarar bana, jirgin shugaban na Najeriya ya isa Landan, a nan ma Muhammadu Buhari ya ga likitoci, ya dawo.
Tafiyar karshe da shugaban kasar ya yi zuwa asibiti ita ce a watan Oktoban bana, an bada sanarwar cewa Buhari ba zai wuce kwanaki 14 a kasar Turan ba.
Kamar yadda Femi Adesina ya yi alkawari, a ranar 13 ga watan Nuwamba, jirginsa ya iso Abuja.
Buhari ya je kasashe 40
Rahoton ya nuna a cikin ziyara da tafiye-tafiye da Muhammadu Buhari ya yi a tsawon shekaru bakwai da rabi, ya je kasashe akalla 40 da ke Duniya.
Shi ma mataimakinsa watau Farfesa Yemi Osinbajo ba a bar sa a baya ba, ya ziyarci kasashe da-dama. Daga ciki har da irinsu Vietnam da kuma Kanada.
APC za ta zarce a mulki?
Bayan Bola Tinubu ya je Chatham House, an ji labari Raji Babatunde Fashola ya fadi yadda za suyi wajen ganin Bola Tinubu ya karbi mulkin kasa a 2023.
Ministan na ayyuka da gidaje ya kaddamar da kwamitinsa da zai taimaka wajen shiga ko ina da nufin kawowa Jam’iyyar APC nasara a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng