Kodai Ka Zabi Jam'iyyar APC A Zabe Ko Kuma Ka Gayawa Aya Zakinta Inji Shugaban Masu Rinjaye
- Doguwa wanda a farkon watan Nuwanban wannan shekarar suka samu sabani da dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano
- Doguwa wanda kuma shine dan majalissa daya tilo da ya taba zuwa majalissa da matansa da 'ya 'yansa dan nya nunawa majalissa yawan kuri'ar da yake da ita
- Shugaban Jam'iyyar APC na jihar Kano yace Koda tsiya ko da tsiya tsiya sai sun ci zaben jihar kano
Kano: Shugaban masu rijaye na majalisar wakili Alhasssan Ado Duguwa ya yiwa magoya bayansa jawabin a wani taro da ya shirya a gidansa dake Kano.
Duguwa wanda yake bayyana kudirinsa da kuma muradinsa ga duk wanda ya kasance yana da katin zabe da dolensa ne ya zabi jam'iyyar APC mai mulki ko kuma ya koka.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun shekarar 1999 bayan dawowar dimukuradiyya Doguwa ke wakiltar Tudun-Wada da Doguwa a zauran majalissar wakilai ta tarayyya, kuma yanzu shine shugaban masu rinjaye na majalissa.
A wani bidiyo mai dakika talatin da jaridar Leadership ta wallafa an jiyo Doguwan nacewa:
"ko ka zabi jam'iyyar APC ko Kaci Ubanka"
Kalamin nasa za'a iya cewa yana kama da wani shagube ko kuma wata magana mai harshen damo idan akai la'akari da wannan maganganu
Na farko;da kuma zata iya yiwuwa Doguwan na magana ne sabida irin aiyukan alherin da yake yiwa mazabar da yake wakilta, da kuma yadda suke nuna masa jin dadin nasu bisa ga wakil nasa
ko kuma zata iya yi wuwa yana nuna zasu yiwa duk wanda bai zabesu ba barazana ba irin ta siyasa ba.
Jami'an tsaro, hukumar zabe, da masu fada a ji a cikin al'umma na kira da yan sisyasa su guji yin kalaman tunziri ko wanda zasu sa al'umma tashin hankali.
Jam'iyyar APC kan Iya Faduwa Zabe Muddin Ba'ai Abinda Ya Kamata Ba - Doguwa
Shugaban Majalisar Wakilai Alhassan Doguwa, ya yi gargadin cewa muddin manyan jam’iyyar APC ba su samu cikakken ikon tafiyar da harkokin jam’iyyar a jihar Kano ba, jam’iyyar za ta iya faduwa a zaben 2023 mai zuwa.
Baya ga haka, jigo a jam’iyyar yana son Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbe ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar domin duba yadda tsohon kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, ke ya yi.
Asali: Legit.ng