Amarya Ta Yanke Jiki Yayin da Ango Ya Fasa Aurenta Ranar Daura Aure, Bidiyon Ya Taba Zuciya

Amarya Ta Yanke Jiki Yayin da Ango Ya Fasa Aurenta Ranar Daura Aure, Bidiyon Ya Taba Zuciya

  • Sabuwar Amarya ta shiga zubda hawaye yayin da wanda ta aura yace ya fasa aurenta a gaban kowa
  • A kan hanyar komawa gida daga Majami'a, Mijin ya yi amai ya lashe ya soke batun aurensu a ranar ɗaura aure
  • Duk da kokarin Amarya da sauran waɗanda abun ya faru a gabansu na shawo kan Saurayin, sam ya ƙi sauraronsu

Wani ɗan Najeriya dake shirin Angoncewa ya bar mutane baki buɗe bayan ya canza shawara, ya fasa auren kyakkyawar amaryarsa a ranar ɗaura aure.

A wani bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya, an jiyo muryar angon na faɗin ya fasa wannan auren, ya bayyana cewa ba zai koma gida da ita ba.

Ranar Aure an rabu.
Amarya Ta Yanke Jiki Yayin da Ango Ya Fasa Aurenta Ranar Daura Aure, Bidiyon Ya Taba Zuciya Hoto: Chidi_obasi
Asali: UGC

Nan take hawaye masu zafi suka fara sauka a kumatun amaryar yayin da ta bi shi tana rokonsa, amma matashin saurayin ya ƙeƙashe kasa kan ba zai canza ra'ayinsa ba.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kama Mijinta Na Rage Zafi Da Wata Yar Magajiya, Bidiyon Matakin da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane

Mutanen da abun ya faru a gabansu sun yi iya bakin kokarinsu na lalubo hanyar maslaha tsakanin masoyan amma duk a banza saboda Saurayin ya ɗau zafi kan matakin da ya ɗauka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika ya ƙi faɗin laifin da aka masa ya jawo ya yanke wannan tsattsauran matakin lokaci ɗaya.

Mutane sun maida martani

Patrick Solomon yace:

"Dan Allah karku kunyata bakinku da suka zo daga kusa ko nesa, ku basu abinci da kayan sha, duk abinda kuka ga dama zaku iya aikata wa bayan auren."

Muhammad Umar yace:

"Ku bar baƙi su ci Shinkafa da nama kafin ku rabu, zaku iya raba hanya idan kuka koma gida, haba meke faruwa ne."

Isi Olie tace:

"Anti ki hau mota ki koma gida abinki, meye na zubda hawaye kuma."

Aliyu Malik yace:

Kara karanta wannan

Gunin Sha'awa: Wata Kyakkyawar Budurwa Ta Bar Mutumin da Bata Sani Ba Ya Kwanta a Jikinta, Hoton Ya Ja Hankali

"Ba haka nan, dole akwai wani ɓoyayyen sirri da ya gano a rayuwarta. Abu ya yi kyau."

Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Lambar Wani Mutumi a Gaban Matarsa, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Ja Hankali

A wani labarin kuma wata kyakkyawar budurwa mai karfin hali ta nemi wani matashin Magidanci ya bata lambarsa a gaban matarsa

A wani bidiyon wasan barkwanci da aka wallafa a soshiyal Midiya, budurwar ta tunkari ma'autan suna tsaye a gefen gidan abinci, ta fara yabon mijin.

Lamarin dai ya ba matar mutumin mamaki matuka musamman bayan sahibinta ya nemi ita ta baiwa budurwar lambarsa, sai cewa ta yi babu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262