Ba Zaku Iya Kashe Rai Ba, FG Ta Umarci a Sauya Wasu Jami'ai Daga Gidan Yari
- Ministan cikin gida ya umarci hukumar kula da gidajen gyaran hali ta sauyawa duk jami'in da ba zai iya kisa ba wurin aiki
- Rauf Aregbesola, ya kuma yaba tare da miƙa kyuata ga Dakarun gyaran hali 25 waɗanda suka jajirce suka dakile harin yan bindiga a Neja
- Ministan ya bayyana cewa duk wanda ya yi kokarin kai hari gidan Yari a tura shi barzahu
Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a ranar Litinin ya umarci hukumar kula da gidajen gyaran hali ta sauyawa Dakaru mata waɗanda ba zasu iya sheke mutum ba, wurin aiki.
Ministan ya ba da wannan umarnin ne a wurin taron bayyana Sabon tambari da Kaki da kuma kaddamar da gidajen ma'aikata, ICT da Motocin Operation a Hedkwatar hukumar dake Abuja.
Legit.ng Hausa ta faminci cewa Jami'ai 25 waɗanda suka nuna kwazo da jajircewa wajen dakile harin 'yan bindiga a gidan Yarin jihar Neja, sun sha yabo da kyauta daga wurin Ministan a wurin taron.
Da yake jinjina wa Jami'an, Aregbesola, ya nuna damuwarsa kan halayyar wasu jami'an gyaran hali, waɗanda ke cika wandonsu da iska idan 'yan ta'adda sun kawo hari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, Gidan yari ya zama wuri mai haɗari a yanzu kuma ya kamata Dakaru su yi harbe tare da sheƙe kowaye ya yi yunkurin kai hari wuraren.
"Bindigu ba kayan wasa bane, an tanade su ne don halaka 'yan ta'adda, duk wani Jami'i da ba zai iya harbi da kisa ba, duk wani Jami'i da ba zai iya fasa kwanyar ɗan ta'adda ba, yana bukatar horo ko a sauya shi."
"Bai kamata yan ta'adda su ji rauni kadai ba, duk wanda ba zai iya harbin da zai kisa ba, idan ba zaku iya korar su ba ku maida su Gidajen Yari na mata."
"Duk wanda za'a aje a manya da matsakaitan Gidan Yari dole su zama masu tsauri. Mun sha fama da harin cikin mutunci ya zama wajibi mu dakatar da irin haka."
- Rauf Aregbesola.
Yace mafi yawan 'yan bindigan dake ta'addanci a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya fursunoni ne da suka tsero daga Gidajen Gyaran hali a jihar Imo.
Ministan ya jaddada cewa duk wanda ya yi yunkurin kai farmaki gidan Yari a tura shi barzahu, kamar yadda Sahara Reporters ta tattaro.
FG Ta Dorawa Gwamnatocin Jiha Laifin Wurga ‘Yan Najeriya a Talauci
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ɗora wa gwamnatocin jihohi laifin kara jefa mutane cikin matsanancin talauci a Najeriya
Ƙaramin ministan tsare-tsare ɗa kasafin kudi, Clement Agba, wanda ya yi wannan zargin yace gwamnoni sun kama hannu abunsu, ba abinda suke yi na tsamo talakawa daga Talauci.
A cewarsa maimakon haka mafi yawa sun fi maida hankali wajen gina muhimman abubuwan more rayuwa a birane, sun watsar da karkara.
Asali: Legit.ng