Da Dumi-Dumi: Wasu Bata Gari Sun Sake Kona Ofishin INEC a Jihar Imo
- Gabannin babban zaben 2023, bata gari na ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
- A ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, mahara sun farmaki ofishin INEC a karamar hukumar Oru ta yamma, jihar Imo
- Harin na zuwa ne yan kwanaki bayan an kai irin harin a ofishin hukumar da karamar hukumar Orlu ta jihar
Imo - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa wasu masu barna da gangan sun cinna wa ofishinta wuta da ke karamar hukumar Oru ta yamma a jihar Imo.
Kwamishinan zabe na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Rikici: Makiyaya da manoma sun yi fada, an kashe mutum 8 har da yada, an kone gidaje 47 a jihar Arewa
A cewarsa, kwamishinan zabe na jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ya kai rahoton cewa an farmaki ofishin hukumar da ke karamar hukumar Oru ta yamma da misalin karfe 4:00 na safiyar yau Lahadi.
Okoye ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Harin ya shafi dakin taro inda aka lalata kujerun ofis da sauran kayayyaki. Sai dai kuma, abun bai shafi sauran wurare masu muhimmanci ba."
Ya kuma tuna cewa a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba, an farmaki ofishin INEC a karamar hukumar Orlu.
Ya ce:
"Gaba daya, wannan shine hari na 7 da aka kai kan cibiyoyinmu a jihohi biyar na kasar nan a cikin watanni hudu da suka gabata.
"Har wayau, hukumar na nuna damuwarta kan illar hare-haren da ake yawan kaiwa cibiyoyinta a fadin kasar kan gudanarwar zabe da harkokin zabe gaba daya."
Ya bayyana cewa an ja hankalin hukumomin tsaro kan wannan lamari na baya-bayan nan da ya faru domin gudanar da bincike da hukunta masu laifin, rahoton Vanguard.
Bata gari sun kona ofishin INEC a jihar Ogun
A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa a watan jiya ne wasu tsagerun mutane suka cinna wa ofishin hukumar zabe ta kasa wuta a yankin Iyana Mortuary da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Harin ya yi sanadiyar lalata ginin hukumar ta INEC bayan maharan sun jefa biredi jike da man fetur cikin cibiyar ta sako-sako.
Asali: Legit.ng