Harin Masallacin Delta: Musulmi Na Fuskantar Barazanar Ƙarewa A Kudancin Najeriya, MURIC
2 - tsawon mintuna
- Farfesa Ishaq Akintola, shugaban kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ya yi kira ga jami'an tsaro su binciko wadanda suka kai hari a masallaci a jihar Delta
- Shugaban na MURIC ya koka kan cewa musulmi a kudancin Najeriya na fuskantar karewa saboda kisan mummuke da ke cigaba a musu
- Akintola ya bada misalin hare-hare da aka rika kaiwa al'ummar musulmi a yankin kudu maso gabashin Najeriya ana halaka su babu gaira babu dalili, yana mai cewa dole a takawa masu kisan birki
Al'ummar musulmi sun fara zama nau'in al'umma da ke fuskantar barazanar karewa a Najeriya, a cewar kungiyar kare hakkin musulmi na Najeriya, MURIC.
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, yayin da ya ke martani kan harin da aka kai babban masallacin Ugelli, jihar Delta a ranar Juma'a, kamar yadda aka wallafa a shafin kungiyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya yi kira ga jami'an tsaro su binciko wadanda suka kai harin kuma su ceto limamin da aka sace yayin harin.
Akintola ya ce:
"Yan bindiga sun sace Malam Muhammadu Sani, limamin babban masallacin Ugheli a jiya. An bindige masu ibada goma sha daya. Yan bindigan sun kutsa masallacin da ke Otovwievwiere Street a Okorodafe a Ughelli misalin karfe 6 na safiyar ranar Juma'a, 2 ga watan Disamban 2022.
"Dole duk mutane masu hankali su yi tir da wannan mummunan abin. Wannan wani shaida ne na harin kiyayya da ake yi wa musulmi a Kudu maso Gabas a baya-bayan nan.
"Idan za a iya tunawa a farkon wannan shekarar, wasu mutane da ba a sani ba sun kashe sakataren kungiyar musulmi na jihar Delta, Mallam Musa Ugasa."
Ya ce wadanda ke ikirarin kirista kadai ake kashewa a kasar nan suna da tambayoyi da za su amsa, rahoton Daily Trust.
Musulmi a kudu maso gabas na fuskanar barazanar karewa - Farfesa Akintola
Ya ce:
"An kashe Sheikh Ibrahim Iyiorji a Isu, karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi a ranar 4 ga watan Satumban 2022. An kashe musulmi bakwai a Orogie, Owerri, jihar Imo ranar 5 ga watan Agustan 2022.
"An kashe wasu musulmi hudu a Umuaka, kusa da Orlu ranar 4 ga watan Afrilun 2021. Kuma, yan bindiga sun kashe wasu musulmi goma sha daya a Fatakwal da Orlu a ranar 20 ga wata Oktoban 2022.
"An kuma kashe wasu musulmi biyar kusa da fitaciyyar kasuwar Abraka da ke Asaba, jihar Delta ranar 15 ga watan Satumban 2017. Abin ba shi da karshe.
"Da Harin ranar Juma'a a babban masallacin Ughelli abin ya yi yawa ... Musulmi sun zama na'in yan adam da ke fuskantar barazanar karewa a dukkan Kudu maso Gabas, dole a dakatar da abin."
Asali: Legit.ng