Yemi Osibnajo Zai Kai Ziyarar Habaka Alakar Kasuwancin Najeriya da Kasar Vietnam
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar Najeriya zai kai ziyara kasar Vietnam
- Osinbajo zai halarci wani zama ne da zai dukufa ga batutuwan da suka shafi kasuwanci da alakar kasar da Najeriya
- Ana kyautata zaton zai dawo Najeriya a ranar Laraba mai zuwa bayan kammala zaman tattaunawar
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo zai bar birnin Abuja a yau 3 ga watan Disamba don zuwa kasar Vitenam, inda zai gana da shugaban kasar; Nguyn Xuân Phúc, mataimakins; Mr. Pho Chu Tich Nuroc da sauran jiga-jigan kasar.
Ziyarar ta Osinbajo a kasar ta Vietnam za ta kara dankon kasuwanci da zumunci tsakanin Najeriya da kasar, PM News Nigeria ta ruwaito.
Idan baku manta ba, a kokarin kulla alakar kasuwanci da kawance, firayinminsitan kasar, Vuong Hue ya kawo ziyara Najeriya, inda ya gana da Osinbajo a 2019.
Alakar kasuwancin Najeriya da Vietnam ta haifar $280m a 2014, inda ta karu zuwa $500m a 2019.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Duk da cewa Najeriya da Vietnam na da alaka mai zurfi tun 1976 ta diflomasiyya, Osinbajo ne shugaba a Najeriya na biyu da ya kai ziyara aiki zuwa kasar bayan tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Ziyarar Osinbajo da wuraren da zai halarta
A wannan ziyarar, Osinbajo zai halarci wani zama da Zauren kasuwanci na Vietnam, inda hakan zai taimaka wajen hada alaka tsakanin ‘yan kasuwan Najeriya da na kasar.
Tare da damammaki masu yawa a fannin noma da fasaha tsakanin Najeriya da Vietnam, tattaunawar da Osinbajo zai halarta za ta mai da hankali ne ga zurfafa alakar kasashen biyu a fannonin kasuwanci.
Rahoto ya bayyana cewa, Osinbajo zai kammala ziyarar aikin ne a ranar Laraba mai zuwa, inji rahoton TheCable.
Buhari ya kai ziyara kasar kasar Nijar
A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya kai ziyara birnin Niamey ta kasar Nijar domin halartar wani taron da aka gudanar na gamayyar kasashen Afrika.
Rahoto ya bayyana cewa, wannan labari na tafiyar Buhari ya fito ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a makonni biyu da suka gabata.
Hakazalika, ziyarar ce Buhari ya halarci wani taron kaddamar da wani littafi da aka wallafa, kana ya kaddamar da wasu ayyukan tituna da aka sanyawa sunansa a kasa.
Asali: Legit.ng