Hukumar Sojojin Nigeria Zata Sauya Yadda Take Kai Hare-Harenta
- Akwai akalla dabarun kai hare-hare da rundunar ke amfani da su kusan guda goma wanda take hada su da sunan yankin da za'ayi aikin
- Shugaban sojojin Nigeria yace a kwanan suna samun nasara akan yan ta'adda a Nigeria musamman yankin gabashin kasar
- Sarakunan Yobe sun yi alkawarin ba da goyon baya ga ayyukan Sojoji da su ke ci gaba da yi a Arewa maso Gabas
Abuja: Rundunar sojin Najeriya na shirin sake duba ayyukanta daban-daban a fadin kasar da nufin ci gaba da yaki da ayyukan ta’addanci.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a Abuja a yayin taron manema labarai na gabanin taron bayan wata hur-hudu da aka shirya gudanarwa a jihar Sokoto.
Taken taron na wannan lokacin shine, “Gyara tare da kimtsa kwararrun Sojojin Najeriya dan sajewa da aiyukan tsaro a Karni na 21.”
Rundunar sojin Najeriya ta ce tana nazarin ayyukanta na fatattakar 'yan ta'adda, 'yan fashi, masu garkuwa da mutane, kungiyoyin 'yan aware, da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka da ke kawo nakasu ga zaman lafiya kasar.
Rundunar ta ce sauye-sauyen da ake samu musamman ma akan yanayin tsaro a kasar nan, na bukatar a sake zage damtse da samar da sabbin dabarun yakar ta'addanci kamar yadda jiridar Vanguard ta rawaito
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Janar Nwachukwu, taron zai sake yin nazari a kan harkokin gudanarwar rundunar sojojin Najeriya tare da yin nazari kan ayyukan da sojojin Najeriya ke ci gaba da yi a dukan shiyyoyi shida na kasar nan.
Mai Yasa Aka Shirya Taron
Taron zai kuma ba da dama ga Hafsan Hafsoshin Sojan kasar nan yin tozali da manyan hafsoshin soja, kwamandojin da sauran manyan kusoshin hukumar dan inganta ayyukan sojoji.
"yace a yayin taron za'a bude kofa dan karbar shawarwari akan hanyoyi da za'a inganta tsaron ƙasa. a don haka, ina nanata kuduri da kudurin hukumar sojoji na tabbatar da kimarmu, jajircewa, ƙware, sadaukarwa, mutuntawa, da horo dan tabttar da martabar kasar mu.
Nwachukwu, yace in zaku lura zaku ga yanzu salon mu ya canja, muna shigo da fareren hula cikin aiyukanmu kuma muna sake karfafawa dakarunmu gwuiwa da samar mu da yanayi mai kyau dan gudanar aiyukansu
ya ce
“Hakan wata nasara xce karkashin jagorancin babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya (CFR) wanda da kokarinsa ne da dabarasa aka kara habaka hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da sauran masu aikata miyagun laifuka a kasar nan”.
Ya ce
“Tare da yunkurinsa na kawo sauyi da sadaukar da kai, sojoji sun ci gaba da fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP a yankin Arewa maso Gabas, wanda hakan ya kai ga halaka manyan kwamandojin ‘yan ta’adda, tare da karya lagonsu. Hakan ya sa ‘yan ta’adda da ‘yan uwansu mika wuya.
Jiragen NAF Sun Ragargaji ‘Yan Ta’addan ISWAP Ana Tsaka da Koya Musu Hada Bama-bamai da Amfani da Makamai
Duk wadannan nasarorin ba za su samu ba idan ba tare da goyon baya da hadin gwiwar ‘yan Najeriya masu bin doka da oda ba, da sauran hukumomin tsaro da shugabannin siyasa da da kuma taimakon wasu kasashen duniya in ji Nwachukwu
Ya ce yayin bude taron, za'a gabatar da lakca mai taken “Yawaitar Makaman Tsaro na Yaki a Najeriya: Kalubale Da ke Tattare da Hakan” wanda Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), tsohon babban hafsan tsaro zai gabatar.
“A ranar 6 ga Disamba, 2022, za a kaddamar da ayyukan hadin gwiwa na rundunar sojojin Najeriya daban-daban da wasu al’ummomi a jihar Sokoto.
Bugu da ƙari, taron zai sake nazarin shawarwarin da aka yanke a taron da manyan hafsan sojin kasar nan suka gabatar sauran batutuwan tsaro. wanda za'ai a ranakun 7 zuwa 8 ga Disamban wannan shekarar da muke ciki.
Asali: Legit.ng