Shugaban CAN Na Jihar Adamawa Ya Zargi Hukumar Alhazai Ta Kirista da Tafka Rashawa
- Shugaban kungiyar CAN ya bayyana zarginsa da cewa, hukumar alhazai ta kirista ta cinye kudaden alhazai a hajjin bana
- Bishop Stephen Mamza ya bayyana yadda ya sha fama a Rome wajen nemawa alhazai wuraren kwana a kasa mai tsarki
- Hukumar ta musanta zarginsa, ta kuma yi karin haske game da aikin hukumar a matakin hajjin bana
Jihar Adamawa - Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Adamawa, Bishop Stephen Dami Mamza ya zargi faruwar tsagwaron rashawa a hukumar alhazai ta kiristoci a jihar, inda ya yi kira ga hukumomin hana rashawa su yi bincike.
Da yake zantawa da namena labarai a birnin Yola ranar Alhamis, Mamza ya yi kira ga sakataren hukumar alhazai Rev. Yakubu Pam ya yi murabus bisa zargin ya cinye kudin wurin kwana da zirganiyar alhazai.
Ya kuma yi zargin cewa, wasu daga cikin alhazai sun kwana daya ne tak a kasa mai tsarki kana aka dawo dasu Najeriya saboda basu da wurin kwana, Daily Trust ta ruwaito.
Zargin da Bishop ya yi kan lamarin hajjin kirista na bana
A cewarsa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Bal ma, sai da na tafi bankin Vatican don ciro kudi a can tare da fara shirin neman wurin kwana ga wasu alhazai saboda a matakin kasa an karbi kudin kuma ba a samar da wurin kwana ba.
"Alhazai sun isa birnin Rome, wasu daga cikinmu basu da dakunan da za su zauna, babu bas babu wani shiri da aka yiwa mutane don zirga a cikin birnin."
Martanin hukumar alhazai kan batun rashawa
Sai dai, da take martani ga batun faston, mai magana da yawun hukumar, Celestine Toruka ta ce, hukumar ba ita ke kulawa da duk wani shirin zirga-zirga da wurin kwana na alhazan ba, New Telegraph ta tattaro.
Daga nan hukumar ta bayyana gaskiyar abin da ya faru da kuma yadda alhazan suke rike da kudadensu a hannayensu ba tare da ba hukumar ta kula da jigilarsu ba.
Ba sabon abu bane a samu tsaiko a lamarin da ya shafi lamunin kudi ba a Najeriya, an sha samun hakan a hukumomi daban-daban na kasar nan.
Ana ci gaba da kai ruwa rana da akanta janar na Najeriya bisa zargin ya sace kudin kasa da aka ajiye a karkashin kulawarsa.
Tuni dai aka ce akanta ya mayar da wasu kudaden, amma har yanzu batun na gaban kotu, kamar yadda rahoto ya bayyana.
Asali: Legit.ng