Sufeta Janar Na Yan Sandan Najeriya Ya Buƙaci Kotu Ta Soke Hukuncin Ɗaurin Wata 3 Da Aka Masa, Ya Bada Dalili

Sufeta Janar Na Yan Sandan Najeriya Ya Buƙaci Kotu Ta Soke Hukuncin Ɗaurin Wata 3 Da Aka Masa, Ya Bada Dalili

  • Usman Baba, shugaban yan sandan Najeriya ya bukaci kotu ta soke hukuncin daurin wata uku a gidan gyaran hali da kotu ta masa
  • IGP Baba, cikin sanarwar da ya fitar ya ce ya samu shawarwari daga bangaren shari'a na rundunar kuma ya garzaya kotu don wanke kansa
  • Sufeta Janar Baba ya ce lokacin magabatansa aka bada umurnin mayar da wanda ya shigar da karar aiki, kuma an dakko hanyar yin hakan don haka shi bai saba umurnin kotu ba

Sifeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya ce ya tafi babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ya shigar da karar neman a jingine karar da aka shigar kansa na zargin saba umurnin kotu.

A karar da ya shigar a ranar Alhamis, Baba ya bayyana dalilan da yasa za a jingine umurnin da kotu ta bada.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Samu Karɓuwa Har Wurin Mayu Da Masu Sihiri, In Ji Dino Melaye

IGP Usman Baba
IGP ya bukaci Kotu ta soke hukuncin daurin wata 3 da aka masa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

Ya ce ya samu shawarwari na shari'a daga kwamishinan yan sanda mai kula da sashin shari'a, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin yan sanda, Olamuyiwa Adejobi, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce ba a nada shi IGP ba a lokacin da aka fara binciken da ake magana a kai da bada umurnin kotu.

Ban saba umurnin kotu ba, ba nine IGP ba lokacin da aka bada umurin - Usman Baba

Kamar yadda Inside Business ta rahoto, IGP Baba ya ce gargadin saba umurnin kotun da aka bada a Nuwamban 2018 da Janairun 2019 kan tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda na wancan lokacin ne, ba shi ba.

Sanarwar ta ce:

"IGP din ya kuma lura cewa tun kafin ya hau mulki, magabatansa sun dauki matakan da suka dace a hukumance don dawo da Patrick C. Okoli, mai shigar da kara, kamar yadda kotun ta bada umurni.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Takardar Tuhuma Guda Ɗaya Da Ake Wa Aminu A Kotu Ta Bayyana

"Kamar yadda ya lura, ana iya ganin hakan ta wasikar da IGP na wancan lokacin ya tura wa hukumar kula da ayyukan yan sanda tun a 2015, kafin umurnin kotun na 29 ga watan Nuwamban 2022, na neman a bada wasikar dawo da mai shigar da kara bakin aiki da masa karin girma kamar yadda kotu ta umurta.
"Don haka, bai kamata a yi batun saba umurnin kotu ba. IGP din ya tabbatarwa yan Najeriya cewa zai cigaba da biyayya ga doka da oda kuma ba zai taba saba umurnin kotu ba."

Shugaban Sojojin Kasa, Manyan Jami’an Gwamnati 3 da Alkalai Suka Daure a Gidan Gyaran Hali

A baya-bayan nan, kotu ta yanke hukuncin daurin gidan yari ga wasu manyan shugabannin hukumomin tsaro a Najeriya.

Na baya-bayansu shine shugaban rundunar yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164