Bayan wata 8 da Aure, Matashi Mai Shekaru 20 ya Saki Matarsa Mai Shekaru 17

Bayan wata 8 da Aure, Matashi Mai Shekaru 20 ya Saki Matarsa Mai Shekaru 17

  • Wani matashin yaro ‘dan Najeriya ya datse igiyoyin aurensa da matarsa mai shekaru 17 kasa da watanni takwas da daura auren soyayyar
  • ‘Dan asalin jihar Imo din ya sanar da karshen aurensa a soshiyal midiya inda yace rayuwar aurensa ce mafi girman kuskure da ya tafka
  • Matashin yace a baya ya fara fatan aurensa ya kasance abunda zai kawo masa farin ciki amma abin sai ya canza zuwa akasin hakan

Wani matashi mai shekaru 20 ya sanar da karshen aurensa da matarsa mai shekaru 17 bayan watanni takwas kacal.

Amarya da ango
Bayan wata 8 da Aure, Matashi Mai Shekaru 20 ya Saki Matarsa Mai Shekaru 17. Hoto daga TikTok/@apito.luxury
Asali: UGC

Ma’auratan masu karancin shekaru wadanda suka yi aure watanni kadan sun rikita soshiyal midiya sakamakon karancin shekarunsu.

Matashin yayi nadamar auren

A yayin wallafa bidiyon auren gargajiyansu a TikTok, ‘dan asalin Mbaise din na jihar Imo ya jajanta cewa gara rayuwarsa bashi da aure fiye da lokacin da yake tare da tsohuwar matarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gara a zauna babu aure fiye da zama da irin ta.
“A saboda haka ne na fito in bayyanawa kowa cewa bamu tare. Nagode da shawarwarin ku.”

- Ya rubuta a kasan bidiyon.

Ya kwatanta ranar aurensa da ranar da tafi kowacce baki a rayuwarsa.

“A tunani na ranar aurena ce zata zama rana mafi farin ciki a rayuwata.
“Ya koma ranar da tafi kowacce bakin ciki a rayuwata.”

A wani bidiyo, yayi bayanin cewa yayi kokarin tattaunawa da tsohuwar matarsa ba sau daya ba, ba sau biyu ba amma ta ki sauarare.

“Auren yarinya mai shekaru 17 shi ne babban kuskuren da na taba yi. Ina mata fatan alheri.”

- Ya rubuta a bidiyon.

Kalla bidiyon:

Soshiyal midiya tayi martani

Nancy Donatus tace:

“A matsayinka na mijinta zaka iya taimakon ta ba tare da ka saketa ba. Wannan yaki ne da imani muke magana a nan ba na zahiri ba.”

Roselyn Rose tace:

“Yadda ka kai shekaru 20 ne abun mamaki. Zai yuwu ta ji abubuwa da yawa a kan ka kuma ta ji tsoron fada maka kafin ku yi aure.”

User4838273210633 tace:

“Babu wani batun abinda ya shafi asiri, ta yuwu yarinya ce kuma gaskiyarta tayi yawa ko kuma tana da wasu shirin a rayuwa fiye da aure ko kuma bata taba son shi ba.”

amaechiezinneprom yace:

“Babu wani batun asiri a nan don Allah, 17 tayi yarinya, wanne aiki gareka a wadannan shekaru ne da zaka iya rike yarinya. Wannan shi ne gaskiya.”

Rashidatahri47@gmail.com tace:

“Yaro idan ka saketa ba matsalarmu bane amma kada ka zo kana zaginta cewa bata yi maka ba. Tayi wa wani namiji ai, abu mai sauki.”

A raba ni da matata kafin hawan jini ya kashe ni, Magidanci

A wani labari na daban, wani magidanci ya gurfana a gaban kotu tare da bukatar a tsinke igiyoyin aurensu.

Magidancin yace bakin cikin matarsa zai halaka shi kuma shekaru aru aru tana aiki amma bai taba sanin albashinta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel