Bidiyon Yar Watanni 19 Tana Jero Sunayen Manyan Biranen Kasashen Duniya Ya Ba Da Mamaki

Bidiyon Yar Watanni 19 Tana Jero Sunayen Manyan Biranen Kasashen Duniya Ya Ba Da Mamaki

  • Wata yar karamar yarinya ta yi fice a dandalin TikTok bayan wani bidiyo ya haskota tana jero sunayen manyan biranen kasashe daidai
  • A wani bidiyo da aka wallafa a TikTok, yarinyar ta cinka daidai inda ta bayyana babban birnin Kenya a matsayin Nairobi
  • Mutane da dama da suka ci karo da dan gajeren bidiyon sun sha mamaki ganin cewa yarinyar ta san cewa a UK take da zama

Bidiyon wata hazikar yarinyar yar watanni 19 wacce ta san sunayen manyan biranen kasashen duniya ya yadu a dandalin TikTok.

Amaya Mwiti wacce tace yarinyar ta san cewa a UK take da zama ita ce ta wallafa dan gajeren bidiyon a dandalin.

Karamar yarinya
Bidiyon Yar Watanni 19 Tana Jero Sunayen Manyan Biranen Kasashen Duniya Ya Ba Da Mamaki Hoto: TikTok/@amayamwiti.
Asali: UGC

Yayin da take amsa tambayoyi a cikin bidiyon mai tsawon sakanni 31 wanda aka wallafa a ranar 30 ga watan Nuwamba, yarinyar ta kasance cike da karfin gwiwa.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Yadda uba ya nade diyarsa cikin jakar leda saboda ta yi masa kashi a jikinsa

Bidiyon karamar yarinya wacce ta san sunayen manyan biranen kasashe

An tambayeta ko ta san inda take da zama, sai ta amsa cewa tana zama ne a UK.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Baya ga sanin cewa tana rayuwa a UK, ta kuma cinka cewa babban birnin Kenya shine Nairobi.

Hatta mahaifiyar yarinyar ta sha mamakin irin kokarin da take da shi duk da karancin shekarunta.

Yayin da take wallafa bidiyon, matar ta yi matmaya:

"Dan Allah ku fada mun ko ka taba haduwa da yar watanni 19 wacce ta san babban birnin kowace kasa, ko harma ta san kasar da take zama."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Suzanne ta ce:

"Wayyo Allah tana da hikima sosai, za ki dunga koya mata Swahili?"

@tamia ta yi martani:

"Na so yadda ta ce Nairobi."

@Becky Holmes ta ce:

Kara karanta wannan

Kanwar Maza: Bidiyon Tarairayar da ‘Yan Uwan Amarya Maza 7 Suka yi Mata Wurin Aurenta ya Kayatar

"Za ta zama yar baiwa a fakaice."

@user7795529467270 ya yi martani:

"Ba ni da nace babban birnin Kenya Mombasa bane."

@Trina Wangari ta ce:

"Muna farin ciki a matsayinmu na goggonin soshiyal midiya."

Bidiyon karamin yaro yana zolayar mahaifiyarsa mai juna biyu

A wani labari na daban, jama'a sun sha mamaki da ganin wayo irin na wani yaro dan shekaru biyu wanda ya tasa mahaifiyar a gaba da zolaya.

Mahaifiyar wacce ke dauke da cikin tagwaye tana motsa jiki kwatsam sai ta hangi yaron a bayanta yana kwaikwayon yadda take tafiya harda sa hannu a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel