Kotu Ta Yanke Wa Sanata Mai Ci Kuma Ɗan Takarar Gwamna Hukuncin Shekara 32 a Gidan Yari
- Babbar Kotun tarayya mai zama a Uyo, ta yanke wa ɗan takarar gwamnan Akwa Ibom a inuwar YPP hukunci kan cin hanci
- Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa (EFCC) ce ta gurfanar da shi kan tuhumar karɓan na goro
- A halin yanzu an tasa Bassey Albert, sanata mai ci zuwa gida Yari inda zai kwashe shekaru 42 da Kotu ta yanke masa
Akwa Ibom - Ɗan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a inuwar YPP, Sanata Bassey Albert, zai shafe shekaru 42 a gidan gyaran hali kan zargin karɓan na goro.
Babbar Kotun tarayya mai zama a Uyo, ranar Alhamis, ta tabbatar da laifin da ake zarginsa kana ta yanke masa hukunci bayan hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da shi.
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa an iza keyar ɗan takarar gwamnan zuwa gidan Gyaran hali da ke Ikot Ekpene a jihar Akwa Ibom domin shafe waɗannan shekaru.
Wane laifi sanatan ya aikata?
Mista Albert, Sanata mai ci dake wakiltar mazaɓar Akwa Ibom ta arewa maso gabas, ya gurfana ne bisa zargin karɓar cin hancin motoci 12 da suka kai miliyan N254m.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanatan ya karɓi wannan tagomashin ne daga wani ɗan kasuwar mai, Olajidee Omokore, lokacin yana kan kujerar kwamishinan kuɗi na Akwa Ibom (2010-2014).
Mista Albert ya kasance mamban jam'iyyar PDP mai mulkin jihar kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa YPP watannin da suka shige.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bayan sauya shekarsa ne, Sanatan ya samu nasarar lashe tikitin takarar gwamnan Akwa Ibom karkashin inuwar YPP a zaben 2023 mai zuwa.
Punch tace Ana hasashen shi ne ɗan takara ɗaya tilo da zai ba takwaransa na jam'iyyar PDP, Umo Eno, ciwan kai a zaben gwamnan jihar Akwa Ibom dake tafe.
A wani labarin kuma kun ji cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya zargi gwamnonin jihohi da cinye kason kananan hukumomi
A ranar Alhamis, 1 ga watan Disanba, shugaba Buhari yace gwamnoni na wawure wasu daga cikin kuɗaɗen da aka tura wa masu rike da gwamnatocin kananan hukumomi.
Buhari, wanda ya yi jawabi daga kasan zuciyarsa, ya tuna yadda wani gwamna da bai ambaci sunansa ba, ya karbi kason ya raba biyu ya sakarwa kananan hukumomi rabi.
Asali: Legit.ng