Wata Mata Mai Tsohon Ciki Ta Kama Danta Mai Shekaru 2 Yana Kwaiwayon Yadda Take Tafiya, Bidiyon Ya Ja Hankali

Wata Mata Mai Tsohon Ciki Ta Kama Danta Mai Shekaru 2 Yana Kwaiwayon Yadda Take Tafiya, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wata mata mai dauke da cikin yan biyu ta cika da mamaki bayan danta mai shekaru 2 ya bi ta a baya tare da kwaikwayon yadda take tafiya
  • Wani dan gajeren bidiyo da Julie Ringwald ta wallafa a TikTok ya nuno yaron yana bin mahaifiyar tasa yayin da take zagaya gidan
  • Sa'o'i 24 bayan wallafa bidiyon a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba, sai gashi ya yadu, ya samu fiye da mutum miliyan 10 da suka kalla a TikTok

Masu amfani da TikTok sun gigita da ganin bidiyon wani yaro wanda ke kwaikwayon yadda mahaifiyarsa mai juna biyu ke tafiya.

A wani dan gajeren bidiyo da Julie Ringwald ta wallafa a dandalin na soshiyal midiya, an gano yaron yana tafiya a bayan mahaifiyarsa rike da kugunsa.

Uwa da danta
Wata Mata Mai Tsohon Ciki Ta Kama Danta Mai Shekaru 2 Yana Kwaiwayon Yadda Take Tafiya, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@julieringwald.
Asali: UGC

A cikin bidiyon mai tsawon sakan 31 wanda ke tashe yanzu haka a TikTok, matar mai tsohon ciki tana zagaya gida ne don motsa jiki lokacin da yaron ya zo tayata.

Bidiyon yaro yana kwaikwayon mahaifiyarsa mai tsohon ciki ya yadu a TikTok

Julie, wacce ke dauke da cikin yan biyu, ta bayyana abun da dan nata mai shekaru biyu yayi a matsayin tsokana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta rubuta jikin bidiyon:

"Ina dauke da cikin yan biyu na watanni 36 sannan dana mai shekaru 2 ya lura da hakan. Lokacin tsokana."

Awanni 24 bayan wallafa bidiyon a TikTok, ya hau sama sosai sannan ya samu mutum fiye da miliyan 10 da suka kalla. Hakazalika ya samu likes fiye da 919k da martani sama da 30k.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin yan TikTok

@Lagrimus Te’o ta ce:

"Ba za ki iya guje mani ba mama."

@Mel Eich ya yi martani:

"Bahaha Shima ya kama dan karamin bayansa."

@Aphrodite Queen ta ce:

"Ya zabi takalo rikici. Yana da kyau da ban dariya."

@user7982272841225 ya yi martani:

"Lol! sarkin tsokana ne ko shakka babu."

Girki da lalatattun tumatiri ya raba saurayi da budurwarsa

A wani labari na daban, wani matashin saurayi ya shata layi tsakaninsa da sahibarsa saboda ta ciyar da ci abinci da ita ba za ta iya ci ba.

Budurwar dai ta rangada masa miya da rubabbun tumatiri sannan ta ciyar da shi inda ita kuma fafur ta ki ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel