Intanet Wahala: Yadda Magidanci Ya Tara N1m Cikin Kankanin Lokaci Bayan Daina Sayen Datan N9k Duk Mako

Intanet Wahala: Yadda Magidanci Ya Tara N1m Cikin Kankanin Lokaci Bayan Daina Sayen Datan N9k Duk Mako

  • Wani magidanci dan Najeriya ya samu fiye da naira miliyan daya bayan ya fasa asusun da ya fara tara kudi tun a ranar 3 ga watan Janairu
  • Matarsa wacce ta ba da labarin ta mika godiya ga maigidan nata, tana mai cewa ya daina siyan datar N9k duk wata sai ya koma tara kudin
  • Matar wacce ta cika da farin ciki ta kuma wallafa takardar da ya bar mata a asusun koda rai zai yi halinsa kafin a bude

Wata yar Najeriya ta jinjinawa mijinta kan dabarar bude wani dan asusun ajiya da yayi don tara yan kudade.

Ta yada bidiyoyi da ke nuna tsabar kudi fiye da miliyan daya da ya samu bayan fasa asusun a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba. Ya tara kudaden ne bayan ya daina siyan datar N9k duk wata.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Murna Yayin da Ta Cika Shekaru 3 Da Fara Sana’ar Soya Kosai, Bidiyon Ya Yadu

Kudade
Intanet Wahala: Yadda Magidanci Ya Tara N1m Cikin Kankanin Lokaci Bayan Daina Sayen Datan N9k Duk Mako Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Matar ta kuma wallafa sakon da mijin nata ya bar mata a cikin asusun, koda ace rai zai yi halinsa kafin su bude asusun bankin na katako.

A cikin rubutaccen sakon mai faranta rai, mijin ya bayyana cewa ya fara tara kudi a asusun a ranar 3 ga watan Janairu. Ya kuma baiwa matar wasu muhimman sakonni, ciki harda bashin da ake binsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gano kudade yan N50, N500 da N1000 baje a kasa bayan an fasa asusun bankin katakon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@iamlacrown ta ce:

"Yanzu da suka karanta wasikar, kuma matar ta san labarin kudin da ke asusun diyar kuma baba yana nan a duniyar nan, hmmmm ina fatan ba zata fara cin tararsa kudade ba."

@sisi_painter87 ta ce:

"Ya fi kama da sakon sai wata rana. Ko menene dalilinsa na maimaita "idan muka bude wannan tare, ki kula da yaranmu da sauransu." Amma dai yayi tunani tunda yana yiwa iyalinsa tanadi. Gaskiya yayi tunani."

Kara karanta wannan

Daga Twitter: Matashi ya jefa kansa a matsala, ya shiga hannu bayan zagin Aisha Buhari

Ya fi yan Yahoo sau dari, budurwa ta wallafa bidiyon saurayinta mai siyar da kosai

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta garzaya shafinta na sadarwa don nunawa duniya bidiyon saurayinta mai siyar da kosai.

Sam bata ji kunyar nunawa masoya irin sana'ar da saurayin nata yake yi ba domin a cewarta ya fi yan yahoo sau dubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel