Mahaifinmu Ne Yayi Watsi Damu: Matashiyar Mai Tallar Lemo Ta Bada Labari Mai Taba Zuciya

Mahaifinmu Ne Yayi Watsi Damu: Matashiyar Mai Tallar Lemo Ta Bada Labari Mai Taba Zuciya

  • Faith matashiyar budurwa ce ‘yar Najeriya wacce ke tallar lemo a tituna domin su samu na abinci tare da taimakon mahaifiyarta wacce bata da miji
  • Yarinyar mai shekaru 15 ta fallasa labarinta mai matukar bayar da tausayi inda tace mahaifinta ne yayi watsi dasu kuma yace baya bukatarsu
  • Ta yuwu yarinyar ta samu taimakon da ya dace daga jama’a ganin cewa mutane da dama sun tabu da irin labarinta mai bada tausayi

Wata yarinya mai shekaru 15 mai suna Faith wacce ke tallar lemu a tituna ta narkar da zukatan jama’a da labarin rayuwarta.

Faith mai tallar lemo
Mahaifinmu Ne Yayi Watsi Damu: Matashiyar Mai Tallar Lemo Ta Bada Labari Mai Taba Zuciya. Hoto daga @mr_original
Asali: UGC

Wani mutumin kirki ya ga yarinyar inda take zaune tana siyar da lemo kuma ya bude baki yayi hira da ita tare da wallafa shi a TikTok.

Kamar yadda Faith tace, tana tallar lemo ne domin su rayu kuma ta taimakawa mahaifiyarta wacce a halin yanzu bata da miji kuma take fafutukar neman na kanta.

A yayin da aka tambayeta inda mahaifinta yake, Faith tace baya bukatarsu kuma saboda haka ne yayi watsi dasu da mahaifiyarta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin da ya ga yadda take magana ba tare da damuwa ba ya taba zuciyar mai daukar bidiyonta, ya tambayeta dalilin da yasa take farin ciki kuma yarinyar tace saboda tana siyar da lemo ne.

Mutumin da ya tausaya mata ya debi kudi har N5,000 ya bai wa Faith tare da alkwarin cewa zai je ya ga mahaifiyarta.

Kalla bidiyon a kasa:

Soshiyal midiya tayi martani

Sirgee01 yace:

“Wannan ba hada shi aka yi ba, ya faru lamarin nan. Wayyo Allah, ina son in dinga wannan amma ba ana bidiyo ba, na san Ubangiji zai min sakayya a gaban kowa idan nayi a sirrance. Ubangiji Kana ji na.”

Ideas Photography yace:

“Idan da zamu iya taimakon jama’a kamar haka da duk abinda zamu iya, jama’a zasu ji wani nau’i na buri. Nayi farin ciki.”

Zarrowdavisongmail yace:

“Na koyi wani abu daga nan yallabai. Nayi tunanin nayi kasa amma zan yi kokarin ganin na sanya wani farin ciki a a cikin kwanakin nan.”

User3863499783503:

“Hmmmmmmm Allah ya albarkace ka gaye… shin wa zai iya dauke wannan kyakyawar yarinyar daga titi. Allah ya sassauto da zukatan hamshakan ‘yan Najeriya.”

Userd5tdknwiw1:

“Naji dadin yadda yace zai gana da iyayenta. Wannan mutumin yana yi wa iyalanta fatan alheri. Allah yayi muku albarka.”

Global Family 2022 yace:

“Murmushin dake fuskanta ya gama magana. Jama’a basu taba manta farin cikin da ka saka su. Godiya muke da halayyar kirkin ka ‘dan uwa.”

Bidiyon mai gasa masara tana turanci kamar baturiya

A wani labari na daban, Bidiyon wata mai gasa masara dake turanci kamar baturiya ya birge jama’a.

A Bidiyon an ga yarinya mai Suna Blessing tana gasa masara inda take hirantawa da wani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel