Bidiyon Mai Gasa Masara Tana Turance Wani Mutum Kamar Baturiya, Ta Ci 279 A JAMB

Bidiyon Mai Gasa Masara Tana Turance Wani Mutum Kamar Baturiya, Ta Ci 279 A JAMB

  • Wata mai gasa masara mai suna Blessing ta burge mutane da hikimar zance irin nata bayan wani mutumi ya yada bidiyonta
  • Mutumin ya shiga hira da budurwar ne a yayin da ya tsaya wurinta siyan masara kawai sai ya nadi bidiyonta saboda burgesa da tayi
  • Ya roki jama’a masu hali da su taimakawa Belessing wajen cimma burinta na karatun likitanci a jami’a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani dan Najeriya, Francis Ngozi, ya je shafin Linkedln don nemawa wata hazikar mai gasa masara mai suna Blessing taimako.

A cewar Francis, Blessing ta samu maki 279 a JAMB kuma tana burin karantar likitanci a jami’a amma rashin kudi yasa take gasa masara tana siyarwa don samun na dogaro da kai.

Blessing
Bidiyon Mai Gasa Masara Tana Turance Wani Mutum Kamar Baturiya, Ta Ci 279 A JAMB Hoto: Linkedin/Francis Ngozi
Asali: UGC

Blessing ta samar da mafita ga matsalar tsaro a arewa

Francis ya ce yadda budurwar ke magana ne ya ja hankalinsa inda ya wallafa bidiyonta na tsawon minti biyar a manhajar LinkedIn tana bayyana abun da ya haddasa rashin tsaro a Arewa da mafita.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Blessing a muhawararta ta bayyana cewa rashin ilimi ne babban dalilin hauhawan rashin tsaro a arewa.

A cewarta, dan arewa mara ilimi tamkar bindiga ne a hannayen yan siyasa masu son zuciya da yan ta’adda domin basu da zuciyar kansu saboda rashin ilimi.

Ta koka cewa yawan yaran da basa zuwa makaranta a arewa suna da yawa idan aka kwatanta da sauran yankunan kasar.

Mafitar da ta bayar na kawo karshen rashin tsaro mai sauki ne - ilimi.

Francis ya ce Blessing na siyar da masara don tallafawa mahaifiyarta. Ya ci gaba da cewa bai kamata a bari irin wannan hakizar yarinyar ta kare a siyar da masara ba.

“Irin wannan kwakwalwa haka, Ina ganin ya kamata a kula da shi. Kada a bari yanayin tattalin arzikin iyalinta saboda gurbatacciyar gwamnati ya hana ta cimma burikanta. Don Allah mu taimake ta,” inji shi.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sabuwar budurwa dalleliya zan auro daga Isra'ila, Jarumin fim mai shekaru 71

Kalli bidiyon a nan.

Jama'a sun yi martani

Anthony Okoye ya ce:

"Tunani mai ma'ana.. tana da sanin ya kamata.
"Ina ganin tallafin karatu zai taimaka wajen inganta ta sosai."

Jennifer Ijeh-Tarila ta ce:

“Ban saurara ba tukuna, kuma son zuwa makaranta da Blessing ke yi abun sha’awa be, amma ana wahala a fadin duniya, a Najeriya da wajenta, kuma ba kowani yanayi bane yake kasancewa saboda rashin kyawun kasa. Ya zama dole na fadi haka kuma na yarda cewa ba a koda yaushe bane kasata take zama matsalar.”

Senior Jegede ya ce:

“Allah ya taimake ta don ta cimma mafarkinta,
“Yara da dama na nan basu ci jamb ba duk da iyayensu na da kudin daukar nauyin karatunsu amma hakan rayuwa take.
“Allah ya albarkace ka yallabai Francis Ngozi.”

Matashi Dan Shekara 27 Ya Koka Da Rashin Samun Aiki Saboda Ana Yi Masa Kallon Karamin Yaro

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

A wani labarin, wani dan kasar China, Mao Sheng, mai shekaru 27 ya bayyana matsalolin da yake fuskanta saboda kankantar halittarsa.

Mutumin wanda aka haifa kuma ya tashi a China, Mao Sheng ya kasance baida aikin yi saboda kankantar jikinsa.

Mao ya ce kamfanoni na kin karbarsa saboda basa so a alakanta su da bautar da karamin yaro saboda yanayinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel