Matashiya Yar Najeriya Ta Zama Likita a UK Shekaru Bayan Ta Yi Aiki a Matsayin Mai Goge-goge

Matashiya Yar Najeriya Ta Zama Likita a UK Shekaru Bayan Ta Yi Aiki a Matsayin Mai Goge-goge

  • Wata yar Najeriya mai suna Odocha Sylvia, wacce ta yi kaura zuwa UK shekarun baya ta bayar da labarinta mai ban mamaki
  • Duk da kasancewarta kwararriyar likita, ta fara aiki a matsayin mai goge-goge a wani shagon siyar da kaya mai suna Primark
  • Bata ji dadin yadda lamarinta ya kasance ba amma mijinta ya karfafa mata gwiwa, ta daure har sai da ta samu sabon aiki a matsayin likita

Wata mata yar Najeriya mai suna Odocha Sylvia ta shawarci mutanen da ke niyan komawa birnin UK da su kasance masu hakuri.

Sylvia ta ba da labarin kanta domin karfafawa jama'a gwiwa da kuma koyar da su muhimmanci hakuri da juriya.

Yar Najeriya
Matashiya Yar Najeriya Ta Zama Likita a UK Shekaru Bayan Ta Yi Aiki a Matsayin Mai Goge-goge Hoto: @iam_kelvinossai
Asali: Instagram

Matashiyar matar kuma uwa ta ce ta koma birnin UK shekaru da dama da suka shige a matsayin likita, amma kuma aikin da ta samu shine na goge-goge.

Kara karanta wannan

Kanwar Maza: Bidiyon Tarairayar da ‘Yan Uwan Amarya Maza 7 Suka yi Mata Wurin Aurenta ya Kayatar

Ta ji babu dadi amma mijinta ya karfafa mata gwiwa sannan ya shawarceta da ta ci gaba saboda yanayin ba zai dore ba har abada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cikin sa'a, shekaru bayan ta kama aiki a matsayin mai goge-goge, sai ta samu aiki a matsayin likita a wani asibiti a UK.

Sylvia ta ba da labarinta

"Barka da safiya. Ina farin cikin dawowa nan. Primark. Nan ne wajen da na fara samun aikina na farko a UK a 2012.
"Ina daukar wannan bidiyon ne saboda na dawo nan bayan shekaru goma a matsayin kwararriyar GP. Ina son karfafawa matasa da ke zuwa UK gwiwa. Ba lallai ne ku samu aikin farko daidai da abun da kuka karanta a makaranta ba.
"UK na da tarin kalubale da farko idan kuka zo amma dole ku zama masu juriya. Wasu lokutan kana bukatar karbar abun da ka samu. na tuna a lokacin na kan ji babu dadi sosai lokacin da nake aiki a matsayin mai goge-goge a nan.

Kara karanta wannan

Daga Daina Siyan Datar N9k, Wani Matashi Ya Tara Miliyan A Asusunsa Na Katako

"Mijina ya kan fada mun yan mata abu ne mai wucewa, ba za ki kasance a nan har abada ba. Na zata kawai so yake ya karfafa mun gwiwa. Magana ta gaskiya dole ka zamo mai alkibla. Kada ka bari hankalinka ya dauke daga mafarkinka."

iam_kelvinossai ya wallafa bidiyon a Instagram dauke da taken:

"Duk da kasancewarta likita, ta fara aiki a matsayin mai goge-goge a UK. Kalli labarfinta. Za ka iya zama abunda ka kake son zama. Abun da kake bukata shine lokaci da jajircewa."

Jama'a sun yi martani

Olaotanoladipupo ta yi martani:

"Shin akwai wata kasa a yanzu baya ga UK? Kawai ian so na tabbatar da cewar sauran kasashe ma na nan a doron kasa."

Olynweke ta yi martani:

"Labarin kamar nawa ne. Zuwana Canada na yi aiki a matsayin mai jiran shago a Walmart tsawon shekaru 5, yanzu ni malamar asibitin ce a A&MH. Ka yarda tda tsarin sannan kada ka daina aikin."

Kara karanta wannan

Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako

Kalli bidiyon a kasa:

Kyakkyawar budurwa ta kama sana'a, shekarunta uku tana suyan kosan siyarwa

Wata kyakkyawar budurwa ta cika da farin ciki da alfahari kan yadda kasuwancinta na soya kosai ke tafiya daidai.

Matashiyar na soya kosan siyarwa tare da yin karatu a lokaci guda domin a ta kai mataki na uku a jami'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng