Yan Sanda Sun Tabbatar da An Yi Harbe-Harbe a Wata Jam'iar Najeriya

Yan Sanda Sun Tabbatar da An Yi Harbe-Harbe a Wata Jam'iar Najeriya

  • Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar harbe-harbe a harabar Jami'ar jihar Kuros Riba ranar Litinin
  • Mai magana da yawun hukumar, SP Irene Ugbo, ta ce lamarin na da alaƙa da kungiyoyin 'yan daba, ɗalibi ɗaya ya jikkata
  • A halin yanzun yana kwance a Asibiti ana masa magani, tace sun samu wasu bayanai daga bakinsa

Cross River - Hukumar 'yan sanda, ranar Talata a Kalaba, ta tabbatar da faruwar harbe-harben bindiga a harabar jami'ar jihar Kuros Riba.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, wanda ta tabbatar da aukuwar lamarin tace an yi harbe-harbe a jami'ar ne ranar Litinin.

Hukumar yan sanda.
Yan Sanda Sun Tabbatar da An Yi Harbe-Harbe a Wata Jam'iyyar Najeriya Hoto: premiumtimesng
Asali: Facebook

Mis Ugbo, Sufuritandan 'yan sanda tace wani ɗalibin ajin ƙarshe a makarantar ya samu raunin harbi lokacin da lamarin ya faru, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Tona Asirin Abinda Yasa Ake Kai Hari da Ƙona Ofisoshin INEC Gabanin 2023

Legit.ng Hausa ta gano cewa a halin yanzu ɗalibin na kwance a wani Asibiti da ba'a faɗi sunansa ba yana karban kulawa a Kalaba, babban birnin jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Me ya haddasa harbe-harbe a cikin jami'a?

Mai magana da yawun 'yan sanda ta alaƙanta faruwar harbe-harben da ayyukan 'yan daba da asiri, inda ta kara da cewa 'yan sanda zasu zakulo duk masu hannu a hukunta su.

Tace:

"Muna sa ido kan ɗalibin a wani Asibiti da ba zamu faɗa ba kuma ya bamu wasu muhimman bayanai. Shi kansa ɗan kungiya ne kuma kunsan matsayar hukumar yan sandan kan 'yan asiri."
"Mun hana dabanci kuma ba zamu zura ido muna kallon wasu su zama barazana ga zaman lafiya ba a babbar birni da sauran sassan jihar nan."

Jaridar Punch ta rahoto cewa tsagerun sun so hallaka shi bayan ya musu turjiyar miƙa wuya da Addar dake hannunsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Bindige Wani Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya

Amma ya tsira ne bayan kawo ɗauki cikin lokaci da dakarun 'yan sanda na sashin yaƙi da yan daba da masu garkuwa da mutane suka yi, waɗanda suka kubutar da shi.

A wani labarin kuma kun ji cewa An Bindige Fitaccen Matashin Mawaki Har Lahira a Jihar Anambra

Bayanai sun nuna cewa Mawakin ɗan kimanin shekara 31 a duniya, Slami Ufeanyi na cikin tafiya a sabuwar motar da ya siya sa'ilin da maharan suka farmake shi kuma suka kashe shi.

Wani aminin abokinsa yace ba zaau iya cewa ga dalilin kai masa hari ba amma suna zargin wani shiryayyen shiri ne da aka kulla masa da nufin ganin bayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel