A Karon Farko, CBN ta Tankawa ‘Yan Najeriya Kan Sukar Sabbin Fasalin Naira
- Bankin CBN tayi martani ga ‘yan Najeriya kan sukar sabon fasalin Naira da suka dinga yi bayan Shugaba Buhari ya kaddamar dasu a makon da ya gabata
- CBN tace an saka su aikin sauya Naira ne cikin kankanin lokaci saboda matsalar da ta kunno kai, don haka dole suka saukaka komai
- Kamar yadda daraktan ayyukan bangaren kudi na bankin ya sanar, sun samu takaitaccen lokaci domin magance matsalar kudin jabu, boye kudi da sauransu
Babban bankin Najeriya yayi bayanin dalilin da yasa aka saukaka sauya fasalin Naira da aka sabun, jaridar TheCable ta rahoto.
Ahmad Umar, daraktan bangaren harkokin kudi na babban bankin Najeriya yayi jawabi a wani taron horarwa na editocin kasuwanci da mambobin kungiyar manema labaran bangaren kudi a Fatakwal ranar Talata.
Umar ya samu wakilcin Amina Halidu-Giwa a taron, wacce ita ce shugaban fannin habaka dokoki na sashen ayyukan kudi na Babban bankin.
A makon da ya gabata, Shugaba Buhari ya bayyana sabbin takardun Naira da aka sauyawa fasali.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai, ‘yan Najeriya masu tarin yawa sun nuna rashin jin dadinsu da ganin sabbin takardun kudin inda suke ta cewa sake musu fenti aka yi ba tsari ba, jaridar The Nation ta rahoto.
A yayin amsa tambaya kan saukaka tsarin sabbin kudin da aka yi, Umar yace babban bankin an bashi takaitaccen lokaci ne domin shawo kan matsalar kudin jabu, boye kudi da sauransu.
“Muna son shawo kan matsala ne kuma da takaitaccen lokaci don yin hakan.”
- Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto yace.
“Sauya fasali ya hada da sauya launi ko girma. Tawadar kanta alama ce ta tsaro.”
Ya dace a sauya fasalin Naira tuntuni
Umar yace sake sauyin fasalin Naira ya dace an dade da yin shi inda aka kara da cewa shekaru 17 kenan tun da aka yi takardun dubu daya, shekaru 21 kenan da aka yi ja N500 yayin da N200 ta kwashe shekaru 22.
Daraktan CBN din yace akasin yadda ake ta yadawa kan cewa bankin zai kara wasu takardun kudi baya da sauya fasalin N1000, N500 da N200, babu wasu kudi da za a kara.
Yace sake fasalin Naira zaI karfafa guiwar ‘yan Najeriya masu yawa da basu amfani da banki wurin komawa amfani da shi.
Kamar yadda yace, hakan zai hana ajiye kudi tsabarsu a gida.
Emefiele ya sanar da sauya fasalin Naira
A wani labari na daban, Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa za a sauya fasalin wasu daga cikin takardun Naira.
Takardun sun hada da N1000, N500 da N200 saboda boyesu da ake yi tare na jabunsu.
Asali: Legit.ng