FG Ta Saka Kamarorin CCTV a Taragwayen Jiragen Kasan Abuja - Kaduna

FG Ta Saka Kamarorin CCTV a Taragwayen Jiragen Kasan Abuja - Kaduna

  • Kafin dawowar kaiwa da kawowar jiragen kasan Najeriya, Gwamnatin tarayya ta saka kamarori a taragwayen jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna
  • An gano cewa, an fara aikin saka kamarorin a ranar Talata kuma har an saka biyu daga cikin ukun da aka yunkura za a saka
  • Sai dai, alamu na nuna aiki bai dawo filin jirgin kasan Idu ba dake Abuja saboda har a ranar Talata cike farfajiyar take da ciyayi

Abuja - Bayan dawo da dage karakainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna, Gwamnatin tarayya ta fara saka manyan kamarori a taragwayen jiragen kasan.

Taragwayen jiragen kasa
FG Ta Saka Kamarorin CCTV a Taragwayen Jiragen Kasan Abuja - Kaduna. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da ministan sufuri, Muazu Sambo, ya sanar da cewa an dage dawo da kaiwa da kawowar jiragen kasan.

A makon da ya gabata jaridar Punch ta rahoto cewa, wasu ‘yan kwangila sun hallara tashar jirgin kasan na Idu domin saka kamarorin da na’urorin bibiyar lamurran jiragen kasan amma sun gaza sakawa.

Hakazalika, Punch ta rahoto a ranar Talata cewa, biyu daga cikin kamarorin farkon da aka je da su an saka su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ziyartar wurin da aka yi a ranar Talata, an gano cewa wasu mutane da ake tsammanin ‘yan kwangila ne suna ta aikin saka kamarorin a taragwayen jiragen kasan.

Sai dai, farfajiyar tashar jirgin kasan har yanzu cike take da ciyayi.

Wata majiya mai karfi a filin jirgin kasan na Idu, ta tabbatar da wannan cigaban inda tace:

“Ana saka DMU a dayan bangaren. Ana saka kamarori uku a kowanne tarago wanda hakan ya mayar da shi shida. Dama tun farko akwai hudu a kowanne tarago amma sun saka uku, biyu a kowanne bangare sai kuma daya a tsakiya.”

Ministan Sufuri ya bayyana lokacin dawo da aikin Jiragen Kasan Abuja zuwa Kaduna

A wani labari na daban, Ministan sufuri, Muazu Sambo ya bayyana cewa jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna zasu koma aiki zuwa karshen watan Nuwamban nan.

Ya sanar da cewa, Gwamnatin tarayya tayi duk wani tanadi da ya kamata na kiyaye rayuka da dukiyoyin fasinjojin da zasu yi amfani da jirgin.

Duk da bai bayyana tsayayyar ranar dawowar aikin jiragen kasan ba, yace nan babu dadewa ‘yan Najeriya zasu cigaba da morewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel