Farashin Litar Man Fetur Zai Iya Tashi Zuwa N400 Kafin Shekara Mai Zuwa
- ‘Yan kasuwa sun bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen sauke man fetur ya tashi a Najeriya
- A yadda abubuwa suke tafiya, mutane za su koma sayen litar fetur a gidajen mai a N400 kafin badi
- Wani shugaba a kungiyar IPMAN yace a yanzu babu tashar da ake saida fetur a farashin tallafi
Abuja - Farashin man PMS wanda aka fi sani da fetur yana iya kai N400 a kan kowane lita a mafi yawan gidajen mai kafin karshen bana.
‘Yan kasuwa sun bayyana cewa za a iya samun karin 100% a kan farashi yayin da ake fama da wahalar fetur, Jaridar Punch ta fitar da rahoton nan.
Manyan dillalai sun ce muddin ba a dauki mataki ba, farashin litar man fetur zai yi ta tashi.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai a Najeriya, Ukadike Chinedu yace masu gidajen mai suna karbar sari N220.
Dole a saida mai a kan akalla N250
Ukadike Chinedu yake cewa tun da ana sayen kowane litar man fetur a kan N220 dole a rika saidawa jama’a a kan akalla N250 domin a samu riba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda Chinedu ya shaidawa jaridar, sai a shirya sayen litar fetur a gidajen mai tsakanin N350 da N400 kwanan nan saboda halin da aka shiga.
Maganar da ake yi yanzu, idan babu mai a tashoshin NNPC, dole ‘yan kasuwa su karbi sari a hannun manyan dillalai, hakan ya sa farashi ya tashi.
Fetur zai iya kai N400 a shekarar nan
“Idan ba ayi da gaske ba, za mu koma sayen litar fetur tsakanin N350 da N400 kafin karshen shekara, lura da yadda abubuwa suke tafiya yanzu.
Idan za ku tuna a baya, na fada maku cewa abin da ake kashewa wajen sauke kowane litar fetur ya kai N400, yanzu dole ba zai yi kasa da N450 ba.
Farashin da gwamnati tace a saida fetur a kan tallafi shi ne N147, amma a yanzu ana zargin babu tashar da ake saidawa ‘yan kasuwa a kan haka.
- Ukadike Chinedu
Rahoton yace akwai wani babban ‘dan kasuwa da ya saye fetur a kan N182, shi ma an yi masa rangwamen ne saboda ya saye tankoki 20 a tashi guda.
Asali: Legit.ng