Gwamna Bagudu Ya Amince da Zaftare Wani Kaso Daga Albashin Ma’aikatan Gwamnati

Gwamna Bagudu Ya Amince da Zaftare Wani Kaso Daga Albashin Ma’aikatan Gwamnati

  • Gwamnan jihar Kebbi ya amince a cire wani kaso daga albashin ma'aikatan gwamnatin jihar don ba su damar samun wadataccen magani da kayayyakin kiwon lafiya a asibiti
  • Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar kwadago ta gabatar da bukatar yin hakan ga gwamnati domin sama musu saukin jinya a jihar
  • Tuni gwamnati ta amince, ta kuma bayyana adadin da za a cire da kuma lokacin da za a fara cire wadannan kudade

Jihar Kebbi - Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya amince a cire kashi 3% na albashin ma'aikatan gwamnatin jiharsa a karkashin shirin inshoran lafiya na Kebbi State Contributory Healthcare Management Agency (KECHEMA).

Wannan batu na amincewar gwamnan na zuwa ne daga bakin mai ba shi shawari kan harkokin yada labarai, Malam Yahaya Sarki a ranar Talata a birnin Kebbi, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU Ta Sake Yin Barazana Game Da Makomar Su Bayan Gwamnatin Tarayya Tai Biris Da Su

Alhaji Safiyanu Garba-Bena, mukaddashin shugaban ayyuka na jihar ya ce, amincewar gwamnan ya biyo bayan bukatar da kungiyar kwadago ta gabatar a jihar.

Bagudu ya amince a zaftare albashin ma'aikata
Gwamna Bagudu Ya Amince da Zaftare Wani Kaso Daga Albashin Ma’aikatan Gwamnati | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya fara tun farko

A tun farko, kungiyar ta kwadago ta nemi a cire kasho 3% daga albashin ma'aiakata tare da tura su ga asusun KECHEMA, People Gazette ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnati ta ce:

"Sanya ma'aikatan gwamnati a kan tsari a matsayin sashen doka zai baiwa hukumar damar samar da hanyoyin kiwon lafiya ga ma'aikatan gwamnati a farashi mai sauki."

A cewar gwamnatin jihar, wannan zaftare albashi zai fara aiki ne daga wannan watan na Nuwamba don turawa ma'aikatar KECHEMA ta fara shirin samar da kayayyakin kiwon lafiya ga ma'aikatan gwamnati.

NARD ta fadi yadda Najeriya ke fuskantar barazanar karancin likitoci, wasu za su bar kasar

A bangare guda, kungiyar likitoci ya bayyana cewa, akwai yiwuwar likitoci 'yan Najeriya 4,000 su bar kasar nan ba da dadewa ba saboda wasu dalilai na mutunta aiki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: ASUU za ta sake komawa yaji aiki saboda wasu dalilai

Kungiyar ta fahimci cewa, akwai likitoci bila-adadin da ke ta ajiye aiki domin neman wani aikin a kasashen waje.

Ana ci gaba da cece-kuce da shiga damuwa kan yadda ma'aikata, musamman lkikitoci ke barin Najeriya domin tarewa a kasashen waje, duk dai saboda aiki a kasar nan bai da dadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.