Kungiyar Malaman Jami'oi Ta Kasa ASUU Tayi Barazanar Kauracewa Aiki Muddin Ba'a Biya Su Albashi Ba

Kungiyar Malaman Jami'oi Ta Kasa ASUU Tayi Barazanar Kauracewa Aiki Muddin Ba'a Biya Su Albashi Ba

  • Har Yanzu Dai ana samun sabani tsakanin gwamnatin Tarayya da Kungiyar malaman Jami'io Takasa Kan Albashi
  • Kungiyar ASUU ta Tabbatar Da Gwamnati Kundirinta Na Dole sai tai amfani UTAS maimakon IPPIS wajen Biyan albashi
  • Kungiyar ASUU ta Janye Yajin Aikin da ta shafe wata takwas ta nayi bayan kotu ta umarce ta da yin hakan

ABUJA: A jiya ne kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta sanar da ‘yan Najeriya game da sabon yunkurinta na kin yin darasi sai an biya membobinta albashi a duk fadin jami'oin kasar.

Kafin Aiwatar da kundirinta ne yasa kungiyar tayi kira ga masu ruwa da tsaki da ‘yan Najeriya masu kishin kasa kira ga gwamnatin tarayya ta biya mambobinta albashin watanni takwas da aka hana su.

Shugaban kungiyar ASUU na jami’ar Ilorin Farfesa Moyosore Ajao ne ya bayyana hakan a wani taro na musamman na reshen kungiyar da aka gudanar a babban dakin taro na jami’ar.

Kara karanta wannan

Rikicin Rashin Albashi: ASUU Ta Sha Alwashin Balle Yajin Aikin da Ba a Taba Yi ba a tarihi

ASUU NGEGE
Kungiyar Malaman Jami'oi Ta Kasa ASUU Tayi Barazanar Kinyin Aiki Muddin Ba'a Biya Su Albashi Ba Hoto: Leadership
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta Rawaito cewa Malaman sun gudanar da tattaki ne a harabar jami’ar kafin daga baya su koma babba dakin dakin taro inda suka yi wa manema labarai jawabi.

Ajao ya ce,

“Bari in tabbatar muku cewa kungiyarmu ta kuduri aniyar ci gaba da jan hankalin gwamnati kan ayyukan da suka rataya a wuyanta duk da irin mugun halin da gwamnati ke mana. Don haka, duk da cewa mun koma aiki a jami’armu, amma rashin sanin halin da gwamnati ta dauka na hana mu albashi na watanni takwas wanda tai kudirin cewa 'ba aiki da biya' wanda zai haifar da rudani.
“A kwanaki masu zuwa, kungiyar mu ita ma za ta mayar da martani ta hanyar yin la’akari da yin amfani da manufar ‘Ba Biya, Ba Aiki’, kuma zaisa tai watsi da aiyukan 'ya'yan kungiyar da ya taru a baya da kuma zuwa gaba, sabida ikirarin da gwamnati tayi na tun farko ta hannun Chris Ngige, cewa mambobinmu ba su yi aiki ba da haka ba biya" .

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulmi Tayi Gargadi ga gwamnonin Arewa kan Marawa Tinubu Baya

“Yana da kyau a lura cewa, kafin dukkan nin kowanne matakin kungiyar kwadago ta bayar da gargadi da kuma kira kan biyawa kungiyar bukuatunta amma abin ya ci tura da saida kungiyar ta tafi yajin aikin. .

"Don haka, muna sanar da jama’a cewa wani sabon rikicin da zai zarce na baya, ya sake kunno kai a cikin Jami’o’in Najeriya domin mambobinmu ba za su iya aiki ba albashi ba,kuma ba za su ci gaba da yin aikin kyauta".

Menene Fatan ASUU

Muna fatan da wannan sanarwa, duk masu ruwa da tsaki, wadanda ke da hannun susa a gwamnati kuma za su yi gaggawar daukar mataki kafin tabarbarewar zaman lafiya da aka samu a harabar makarantunmu a fadin kasar.
"Kungiyarmu da membobinta sun kasance cikin alhini da kuma kokawa game da halin da gwamnati ta jefa ilimi da irin yanayin da kasa ta shiga na halin ni'yasu."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarin Gwamnan Arewa, Ya Sha Da Kyar

Ya kara da cewa:

"A matsayinsu na kungiyar masu bin doka da oda, sun bi umarnin kotu wanda ya umarce su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu yayin da ake ci gaba da sauraren wannan batu. To sai dai kuma bayan da suka koma yajin aikin kuma abin ya ba su mamaki, gwamnati ta yanke shawarar cewa za a biya mambobinsu rabin albashi na watan Oktoba, 2022.ne kawai"

Ya kara da cewa:

"Wannan ci gaban ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma kungiyar za ta yi turjiya".

Yana mai cewa

"Malaman jami’o’i ma’aikata ne na yau da kullun . Haka kuma dokar kasa ta bayyana a kan haka ko basuyi aiki ba za'a biyasu; kamar yadda kotun ma’sana'atu ta sanar "

Asali: Legit.ng

Online view pixel