Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Sanata Na Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Adamawa

Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Sanata Na Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Adamawa

  • Wata kotu a jihar Adamawa ta soke tikitin takarar majalisar dattawa na kakakin majalisar dokokin jihar
  • An soke tikitin ne bayan da aka shigar da karar da ke kalubalantar shigowar wani ma'aikacin gwamnati harkar siyasa
  • Ba wannan ne karon farko da kotu a kasar nan ke soke zaben fidda gwani ko korar dan takara ba, an sha yin hakan sau da aywa

Jihar Adamawa - Kotun tarayya mai zamanta a birnin Yola ta soke tikitin takarar sanatan Adamawa ta tsakiya a jam'iyyar PDP da aka ba kakakin majalisar dokokin jihar, Aminu Iya-Abbas a zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Mai shari'a Abdulazez Anka, a hukuncin da ya yanke daga karar da Muhammad Modibbo ya shigar kan PDP da wasu mutum hudu ya bayyana soke tikitin na takarar sanata a jihar, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Machina Matsayin ‘dan Takarar Yobe ta Arewa

Mai shari'a ya kuma bayyana cewa, shigowar shugaban gudanarwar jami'ar jihar Adamawa, Alhaji Auwal Tukur cikin harkar siyasa a lokacin zaben fidda gwanin ya saba da dokar zaben ta 2022.

An karbe tikitin takarar sanatan Adamawa ta tsakiya
Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Sanata Na Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Adamawa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dalilin da yasa aka soke tikitin sanatan Adamawa ta tsakiya

Bisa hukuncin kotun, yanzu babu tikitin takarar sanatan Adamawa ta tsakiya a zaben 2023 mai zuwa, rahoton DailyPost.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba wannan ne karon farko da kotu ke soke zaben fidda gwani ko kwace tikitin takara ba, an sha yin hakan a jihohi da yawa a Najeriya.

Kakakin majalisar ya banke Tukur, dan tsohon shugaban PDP, Babagana Tukur da wasu 'yan takara biyar da suka hada da Barista D.D Azura, Muhammad Modibbo, Ibrahim Mustapha, Ibrahim Abubakar da Hon. Abdullahi Prambe.

Da yake kalubalantar zaben, Modibbo ya shigar da kara, inda ya nemi bahasin ko Auwal Tukur a matsayinsa na ma'aikacin gwamnati ya cancanci yin takara a karkashin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Aisha Binani Ta Koma Mahaifarta Bayan Nasarar Da Ta Samu a Kotu, Ta Samu Kyakkyawar Tarba Daga Masoya

An tabbatar da soke zaben fidda gwanin PDP a Zamfara

A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da PDP ta daga kan soke zaben fidda gwaninta a jihar Zamfara.

A baya kotu ta soke zaben fidda gwanin PDP bisa zargin an yi rashin gaskiya tare da umartar jam'iyyar ta sake gudanar da zaben.

A bangare guda, an sake zaben, wanda daga nan ma aka sake shigar da karar da ke kalubalantar sake zaben da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel