"Don Allah Ku Yafe Wa Ɗanmu", Iyayen Aminu Azare Sun Roki Aisha Buhari Ta Yi Masa Afuwa
- Iyaye da yan uwan Aminu Azare, dalibin jami'ar FUD da jami'an tsaro suka kama kan zargin 'zagin' Aisha Buhari sun roki matar shugaban kasar ta yafe wa dansu ta sake shi
- Shehu Baba-Azare, kawun Aminu ya ce ba su san an kama shi ba bayan kwana biyar da faruwar abin lokacin da abokin karatunsa ya musu waya cew a bai san inda ya ke ba
- Baba-Azare ya ce mahaifin Aminu ya fada masa cewa ya kira shi ya fada masa an kama shi an kai shi Abuja, an masa duka a gaban matar shugaban kasa an kuma kai shi wani wuri an rufe shi
Iyayen dalibin jami'ar tarayya da ke Dutse, Aminu Azare, wanda aka kama kan zargin matar Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, 'ta ci kudin talakawa ta koshi' sunyi kira ga first lady din ta yafe wa dansu ta sake shi, rahoton Premium Times.
An kama Mista Azare, dalibin ajin karshe da ke karanta kula da muhalli da ilimin kimiyyar nazari kan guba (Environmental Management and Toxicology) a jami'ar ne bayan rubutun da ya yi a shafinsa na Twitter a watan Yuni kan zargin Aisha Buhari, ya bazu bayan yan watanni.
Ya lika hoton Aisha Buhari a jikin rubutun da ya wallafa a Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da ya ke magana da BBC Hausa a ranar Litinin, Shehu Baba-Azare, kawun dalibin da aka kama, ya ce iyalan suna rokon matar shugaban kasar ta yi wa dan su afuwa.
Ya ce yan uwansa ba su san an kama shi ba sai bayan kwana biyar da faruwar lamarin, abokin karatun dansu ya fada musu, cewa bai gan shi ba na kwanaki.
Ya ce an kama Aminu a ranar 17 ga watan Nuwamba an kai shi Abuja, inda aka tsare shi kuma aka rika azabtar da shi a gaban Aisha Buhari, Sahara Reporters ta rahoto.
Kawun ya ce:
"Mahaifinsa bai da masaniya kan kama shi ... da safiyar ranar Litinin, Aminu ya kira mahaifinsa ta lambar jami'in tsaro ya sanar da shi jami'an tsaro sun tsare shi a Abuja. Ya ce an kai shi gidan gwamnati, an masa gargadi tare da dukansa a gaban matar shugaban kasa, kafin aka kai shi wani wurin da bai sani ba aka rufe shi.
"Daga baya mahaifin ya sanar da ni cewa mahukunta jami'an (Jami'ar Tarayya da ke Dutse) sun kira shi sun ce ba su san maganar kamen ba."
Muna rokon Aisha Buhari ta duba Allah ta yafe wa dan mu Aminu ta sake shi - Azare
Kawun ya ce yan uwan suna cikin rudani game da lamarin.
Azare ya ce:
"Tabbas, mun damu. Akwai irin wadannan kamen da har yanzu ba a warware ba. Muna rokon ta ta yafe wa dan mu saboda ita ma mahaifiya ce. Ta yafe masa ta manta da sbin. Muna rokon ta."
Martanin Kakakin Aisha Buhari Kan Kama Aminu Azare
A lokacin da Premium Times ta tuntubi mai magana da yawun Aisha Buhari, Aliyu Abdullahi, ya ce yana cikin taro.
Bai kuma amsa sakon tes da aka tura masa game da batun ba daga baya.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International cikin wata sanarwa da ta fitar ta bukaci a saki dalibin.
Ta ce
"Amnesty International ta bukaci hukumomi su sake shi daga tsarewar da aka masa ba bisa ka'ida ba kuma su tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ake zargi da azabtar da shi da cin zarafinsa da aka yi a gaban kotu"
Jami'an tsaro sun kama dalibin da ya ce Aisha Buhari ta ci kudin talakawa - Majiya
Jami'an tsaro da ake kyautata zaton yan sanda ne sun kama Aminu Muhammad Azare bisa yin rubutu yana sukar matar shugaban Najeriya, Aisha Buhari, a Twitter.
Ya yi rubutun ne tun a watan Yunin 2022 amma a baya-bayan nan ya bazu.
Asali: Legit.ng