Ku Sa Ido Sosai a Kan Kayayyakinku, Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci Yan Najeriya Da Za Su Kasashen Turai
- A ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, FG ta bayar da muhimmiyar shawara ga yan Najeriya masu zuwa kasashen Turai
- An bukaci yan Najeriya masu zuwa Amurka, Birtaniya da sauran kasashen Turai da su saka idanu sosai a kan kayayyakinsu musamman kudi da fasfot
- Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayar da wannan sanarwar a babban birnin tarayya Abuja
Abuja - Gwamnatin tarayya ta shawarci yan Najeriya da ke tafiya Birtaniya, Amuka da wasu kasashen Turai da su kula da yanayin tsaro, jaridar The Nation ta rahoto.
FG ta bayyana cewa ta damu matuka da yadda matafiya yan Najeriya ke rasa kudade, fasfot da kayayyakinsu a wadannan kasashe biyu.
Ana yiwa yan Najeriya fashin kudi, fasfot da kayayyakinsu
Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayar da shawarar a wajen wani taro na gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Vanguard ta nakalto ministan na cewa:
“An ja hankalin gwamnati cewa ana yiwa matafiya yan Najeriya masu zuwa Amurka da wasu kasashen Turai fashin kayayyakinsu musamman kudi da fasfot dinsu.
“Wadanda abun ya ritsa da su na baya-bayan ne sune matafiya zuwa kasar Birtaniya, wadanda yawancinsu an kwashe masu kayayyakinsu ne a manyan shagunan siyar da kaya, musamman a babban titin Oxford.
“Saboda haka muka yanke hukuncin shawartan yan Najeriya da ke tafiya zuwa Birtaniya da Amurka da su kula sosai don gudun sace masu kayayyakinsu.
“Wannan ba shawarar ku ta tafiya bace. Bayar da irin wannan shawarar hakkin ofisoshin jakadanci, manyan hukumominmu da kuma ma'aikatar harkokin waje ne.
“Kawai dai shawara ce ga ‘yan Najeriya wadanda za su iya ziyartan yankunan da abun ya shafa a duniya.”
Za a yi bankwana da Dubai: Za a fara kera gwala-gwalai a Kano, gwamnatin tarayya
A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihar Kano na gab da zama cibiyar kera gwala-gwalai yayin da ake shirin kaddamar da kasuwar gwal a 2023.
Kamar yadda ministan ma'adinai da karafa, Mista Olamilekan Adegbite ya bayyana, an fara horar da mutanen da za su dunga kera dankunnaye, awarwaro abun wuya da sauran kayan ado na gwal.
Asali: Legit.ng