Hotunan Flossie, Mage Mafi Tsufa a Duniya Wacce Ta Kusan Shekaru 27
- Kundin tarihi na Guinness ya ayyana cewa, mage mafi dadewa duniya sunanta Flossie kuma daga kasar Burtaniya take
- Flossie ta rayu akalla shekaru 26 da kwanaki 329, wanda daidai kwanakin suke idan kwatanta da shekaru 120 ga dan Adam
- Wannan halitta ta rayu tsawon shekaru duk da kuwa ta zauna a hannun jama'a da dama, daga gida zuwa gida
Mage mafi dadewa a duniya inji kundin ajiye tarihi na Guinness 'yar shekaru 27 ne, kuma daga kasar Burtaniya.
Magen mai suna Flossie ta shekara 26 da kwanaki 329 a duniya, wanda yake daidai da shekaru 120 da dan Adam zai yi a duniya, lamarin da ya ja hankalin jama'a.
Kamar dai sauran dabbobi masu jini a jika kuma suke kan ganiyar samartaka, wannanr kyanwa na nan cikin koshin lafiya, amma ba ta gani sosai kuma ta rasa jinta kadan.
Ya rayu a gidaje daban-daban
Flossie, wacce aka ce tana kaunar abinci da kuma kwanciya a jikin mutane, ta rayu rayuwar jin dadi a gidajen mutane da dama.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai wannan dabba a yanzu, Vicki, ta bayyana cewa, duk da kyanwar ba ta gani da kyau, tana iya fahimtar komai da ke zagaye da ita a cikin gida.
Vicki ta ce, Flossie ba ta da sana'ar da ta wuce kwanciya tare da sharar bacci, ko kuma cin abinci mai dadi da ta saba samu.
A cewarta:
"Ba ta tsallake tayin abinci mai dadi ko kadan."
Farin shigar Flossie kundin tarihi ya fara ne a watan Agustan 2022, lokacin da aka mika ta ga cibiyar kula da maguna ta Cat Protection a Burtaniya.
Wannan mage dai ta fara shiga hannun mutane ne a 1995, a lokacin da take karama tana gararanba a gari.
Ta sha sauyin iyayen gida, daga wannan hannu zuwa wannan har ta kai ga inda take a yau dinnan.
Bera ya samu lambar yabo a kasar waje
A wan labarin mai kama da almara, an ba wani bera lambar yabo bisa aiki tukuru da ba da gudunmawa a karkar tsaro.
Wannan bera ya yi ayyuka a wasu kasashen waje, inda yake taimakawa wajen gano inda aka dasa bam a kasa.
Mutane da dama sun ji mamakin irin aikin beran, kuma gashi aka bashi lambar yabo mai girma.
Asali: Legit.ng