Gwamna Fintiri Ya Sha da Kyar Yayin da Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarinsa
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya tsallake rijiya da baya yayin da hatsari ya rutsa da Ayarin motocinsa a Yola
- Bayanai sun nuna cewa wata Tifa ce ta yi kan motar da gwamnan ke ciki amma Allah ya tsare, direban ya kautar da ita
- An ce dakarun 'yan sanda biyu ne suka samu raunuka, ɗaya ya farfaɗo yayinda ɗayan ke kwnace Likitoci a kansa
Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya shallake rijiya da baya yayin da wata babbar Mota ta murkushe biyu daga cikin motocin ayarinsa ranar Asabar.
A cewar wani Ganau, lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan gwamnan da wasu kwamishinoninsa sun shiga Motas Bas Marsandi da aka gama wani ɗaura aure a Masallacin Agga dake yankin Dougirei highbrow, Yola.
An ce babbar Motar ta shawo gangara a Titin lokacin da ta yi awon gaba da Motocin biyu, 'yan sanda biyu suka jikkata Insufekta Madu da Sajan Musa.
Yadda lamarin ya faru
Wani mazauni, Muhammad Dougirei, ya ce ba zato ba tsammani babbar Motar ta keto da gudun tsiya ta tunkari Ayarin motocin gwamnan, ana tunanin ta sha karfin direban.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace jami'an tsaro dake kan hanyar suna ba da hannu ba su ankara ba suka yi ta kansu ganin yadda motar ta kutto.
Dougirei ya shaida wa wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci wurin cewa Direban ne ya yi ƙoƙarin shan kwana da motar yayin da ta tunkari Bas ɗin da gwamna Fintiri ke ciki.
A cewar mutumin sakamakon haka ne Babbar motar ta yi ciki da Motar Babban sakataren ma'aikatar siyasa da harkokin tsaro da kuma wata 406 mai ɗauke da yan jarida da 'yan sandan da suka ji rauni.
Ya ƙara da cewa nan take jami'an sanda suka kewaye dattijon Direban da duka suka haɗa da wani mai basu hakuri, daga bisani suka jefa shi Mota zuwa Caji Ofis ɗin Jimeta.
Haka nan gwamna Fintiri, wanda Allah ya yi wa gyaɗar dogo ya tswatarwa Direban bayan jikinsa ya gaya masa sannan aka tafi da shi, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Wata majiya tace Insufektan da lamarin ya shafa har yanzun bai farfaɗo ba a sashin kula na babban Asibiti na musamman yayin da Sajan ɗin ya fara gane inda yake.
"Hatsarin ya faru a kan idanun mutane, Allah ne ya tseratar da gwamna da sauran mutanen dake tare da shi a Bas din. Ku duba yadda Dakaru suka yi takansu kafin Tifar ta yi burki da Motocin biyu."
Da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya sha alwashin dawowa gare mu bayan ya tattaro bayanan abinda ya faru.
Ku Yafe Mun Kura-Kuran da Na Tafka a Zamanin Mulkina, Masari Ya Roki Katsinawa
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Katsina ya roki Al'ummarsa su yafe masa kura-kuran da ya aikata a zamanin mulkinsa
Aminu Masari, wanda wa'adin mulkinsa zai ƙare a watan Mayu, 2023 ya yi wannan roko ne a wurin kaddamar da kwamitin kamfen jam'iyyar APC na jiharsa.
Sai dai yace akwai waus mutane da basu gode wa Allah kan duk abinda ya basu a gwamnati, inda yace wasu ma basu samu abinda suke so ba ko kaɗan.
Asali: Legit.ng