Kaduna: 'Yan Ta'adda Sun Halaka Manoma 15 a Wasu Yankuna

Kaduna: 'Yan Ta'adda Sun Halaka Manoma 15 a Wasu Yankuna

  • 'Yan ta'adda a jihar Kaduna sun halaka wasu manoma 15 a kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Kajuru a jihar
  • Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida, ya sanar da cewa, a karamar hukumar Giwa kadai an halaka manoma 11 har lahira
  • Sauran hudun kuwa an halaka su ne sakamakon farmakin da aka kai musu a kananan hukumomin Birnin-Gwari da Kajuru

Kaduna - Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kisan wasu manoma 15 da ‘yan ta’adda suka yi a kananan hukumomi uku na Giwa, Birnin-Gwari da Kajuru a jihar.

'Yan bindiga
Kaduna: 'Yan Ta'adda Sun Halaka Manoma 15 a Wasu Yankuna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A wallafar da kwamishinan yayi a Facebook, ya kara da cewa, hare-haren sun yi sanadin jigata wasu mazauna kananan hukumomin da abin ya shafa.

Aruwan ya ce a karamar hukumar Giwa kadai, an tabbatar da mutuwar mutane 11 a yankin, yayin da a Birnin-Gwari da Kajuru aka tabbatar da mutuwar mutum biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya Za tayi Karin Albashi, An Bayyana Ma’aikatan da Abin Zai Shafa

A cewarsa, wadanda 'yan ta'addan suka kashe sun hada da Abdullahi Musa, Adamu Musa, Aminu Nasiru, Adamu Ibrahim, Ya’u Usman Ladan, Yunusa Saidu, Salisu Abdulrahman, Fati Usman, Yakubu Ya’u, Marwanu Ibrahim da wata gawar da ba a tantance ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a karamar hukumar Kajuru da: Idon Bonos, da Aston Namaskar yayin da ‘yan ta’addan suka halaka Salisu Mai Tireda, da Mohammed Maikaba a Birnin Gwari.

Kwamishinan ya ce:

"Cike da takaici, gwamnatin jihar Kaduna tana mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su a kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Kajuru.
“Jami'an tsaro sun sanar da gwamnati cewa ‘yan bindiga sun kai hari a Rafin Sarki a karamar hukumar Giwa, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 11."

Hakazalika, wasu ‘yan bindiga sun halaka mutane biyu a Damari, karamar hukumar Birnin Gwari. Wadanda aka halakan sun hada da Salisu Mai Tireda da Mohammed Maikaba.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: An kaure tsakanin 'yan Kudu da Arewa a Twitter bayan gani hotunan man da aka hako a Arewa

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana matukar takaicinsa kan sabbin hare-haren da ake kaiwa jama'a yayin da yake jajanta wa iyalan wadanda abin ya ritsa dasu tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.

“Gwamnan ya kara da yin addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda sukasamu raunika. Gwamnati na kira ga jami’an tsaro kan wadannan abubuwan da ke faruwa da sauran bangarorin da suka shafa"

- Kwamishinan ya kara da cewa.

'Yan bindiga sun halaka 'yan sanda 3, sun yi garkuwa da attajiri

A wani labari na daban da Legit.ng ta kawo, wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kwantan bauna kan ayarin motocin wani hamaskin mai kudi inda suka sheke 'yan sanda 3.

An gano cewa, sun hau har gadar sama inda suka bude wuta kan ayarin motocin, lamarin da ya rikita masu ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel