ASUU Ta Yi Barazanar Komawa Yajin Aikin Saboda Biyan Mambobinta Rabin Albashi

ASUU Ta Yi Barazanar Komawa Yajin Aikin Saboda Biyan Mambobinta Rabin Albashi

  • Kungiyar malaman jami'a ta bayyana yiwuwar sake komawa yajin aiki saboda wasu dalilai da suka bullo a watan jiya
  • Kungiyar ta sha mamaki yayin gwamnati ta biya mambobinta rabin albashi bayan dawowa daga yajin aiki
  • ASUU ta yi watanni takwas tana yajin aiki, lamarin da ya kawo cikas ga lamarin karatun jami'a a kasar nan

FCT, Abuja - Kungiyar malaman jami'a (ASUU) ta yi wata kwarya-kwaryar zanga-zanga kan rikicinta da gwamnati da kuma rashin biyansu cikakken albashi a watan da ya gabata.

ASUU ta ce wannan zanga-zanga sun yi ta ne don nuna damuwa ga yadda ake yiwa lakcarori rikon sakainar kashi da kuma alanta tsarin 'ba aiki ba albashi a kansu', da kuma tursasa su su koma bakin aiki ba tare da samun hakkinsu ba.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Kungiyar ta ce, matukar gwamnati ta gaza biya musu bukata, to tabbas majalisar zartaswarta za su koma su sake zama tare daukar matakin da ya dace, AIT ta tattaro.

ASUU za ta koma yajin aiki saboda wasu dalilai
ASUU Ta Yi Barazanar Komawa Yajin Aikin Saboda Biyan Mambobinta Rabin Albashi | Hoto: ait.live
Asali: UGC

Ya kamata 'yan Najeriya su sa baki gwamnati ta ci alkawuranta ga ASUU

Da yake jagorantar gangamin zanga-zangar a farfajiyar jami'ar Abuja, shugaban ASUU na yanki, Kassim Umaru ya yi kira ga 'yan Najeriya da su takura gwamnatin tarayya ta biyawa kungiyar bukatunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASUU ta kuma yi kira ga shugaban majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila da ya cika alkawarin da ya shiga tsakaninsa da kungiyar, Sahara Reporters ta ruwaito.

Hakazalika, kungiyar ta bayyana cewa, ba za ta hakura kan bukatarta ba har sai gwamnati ta biya su kudaden da suke binta tun daga 2020 zuwa yanzu kamar yadda yake a yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Idan baku manta ba, kungiyar malaman jama'a ta shafe watanni takwas tana yajin aiki a shekarar nan, lamarin da ya jawo koma-baya a fannin ilimi a kasar nan.

Kungiyoyin malaman jami'a na ci gaba da zanga-zangar nuna damuwa ga yadda gwamnati ta gaza cika alkawuranta ga kungiyar.

A makon nan ne kungiyar reshen jihar Jigawa ta yi zanga-zanga don nuna damuwa ga biyan mambobinta rabin albashi.

Kungiyar ta ce, gwamnati ta saba ka'idojin aiki na gida Najeriya da na kasa da kasa a wannan karon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.