Mambobin ASUU Sun Yi Zanga-Zangan Lumana A Jigawa Kan Biyansu Kan Zaftare Musu Albashi

Mambobin ASUU Sun Yi Zanga-Zangan Lumana A Jigawa Kan Biyansu Kan Zaftare Musu Albashi

  • Mambobin kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, na Jami'ar Tarayya ta jihar Jigawa sun yi zanga-zangan lumana kan biyansu rabin albashi
  • Malaman jami'o'in sun yi tir da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na neman mayar da su ma'aikatan wucin gadi duba da cewa su cikakkun ma'aikata ne
  • Dr Bashir Yusuf, shugaban ASUU na FUD ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya malaman sauran albashinsu da allawus duba da cewa yajin aikin da suka yi kan ka'ida ne

Dutse, Jigawa - Kungiyar ma'aikatan jami'o'i, ASUU, reshen Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa ta nuna kin amincewarta da mayar da ma'aikatanta tamkar na wucin gadi, rahoton Channels TV.

Zanga-zangan ASUU a Jigawa
Mambobin ASUU Sun Yi Zanga-Zangan Lumana A Jigawa Kan Biyansu 'Rabin Albashi'. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

Biyan malaman jami'a tamkar ma'aikatan wucin gadi ya saba wa doka - Dr Yusuf

Shugaban na ASUU a FUD, Dr Bashi Yusuf ya bayyana hakan yayin zanga-zangan, yana mai cewa hakan ya saba dokokin aiki, da dokokin kwadago na kasa da kasa da aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun karya lagon 'yan bindiga, sun ceto mutane da yawa da aka sace a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Bashir ya yi bayanin cewa malaman jami'o'in ma'aikata ne da aka dauke su aiki na cikakken lokaci wadanda ayyukansu ke da wasu banbance-banbance da wasu ma'aikatan gwamnati masu zuwa aiki karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.

A cewarsa, koyarwa a jami'a cikakken aiki ne da ya kunshi koyarwa, bincike da ayyukan yi wa al'umma hidima, ya ce:

"Ba za a rika biyan mu na wucin gadi ba ko rabin albashi kan yajin aiki da muka yi bisa tsarin doka duk da mun dakatar."

Kungiyar ASUUn ta FUD, ta yi tir tare da nuna amincewarta da mayar da malaman ma'aikatan wucin gadi kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya su cikakken albashinsu da allawus.

Malaman na FUD sun yi tattaki na lumana daga Cibiyar Dalibai zuwa ginin Majalisar Jami'ar rike da takardu masu dauke da rubutu daban-daban don isar da sakonsu, Radio Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Malaman suna kira ne a samarwa dalibai da malaman yanayi da ya dace domin koyarwa a dukkan jami'un kasar nan.

Wakilin Legit.ng Hausa ya samu ji ta bakin wani ma'aikacin jami'ar tarayya ta Dutse, kuma mamba na kungiyar ASUU dangane da zanga-zangar lumanar da kungiyar ta gudanar.

Ma'aikacin da ya bukaci kada a kama sunansa saboda wasu dalilai ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa kungiyarsu ta yi wannan zanga-zanga ne don jawo hankalin gwamnati kan hakokinsu da ba a biya su ba duba da cewa aikin da suka bari a baya sun dasa kansa daga yanzu kuma dama yajin aikin bisa ka'ida na neman hakokinsu suka yi.

Sai dai ya ce a karshe hukuncin da kotun daukaka kara za ta yanke shine zai zama abu na karshe amma yana fatan gwamnatin za ta yi abin da ya dace ta biya su hakokinsu.

Kalamansa:

"Eh toh, kamar yadda abin ya faru, kotu ta umurci mu koma bakin aiki, mun kuma dawo amma sai muka ga an yi mana biyan albashi irin ta ma'aikatan wucin gadi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Amince Da Karin Albashi Ga Wasu Ma'aikata

"Hakan ba dai-dai bane domin duk abin da muka baro a baya yanzu mun dora a kansa kuma za mu yi baki daya kuma dai mu ba ma'aikatan wucin gadi bane.
"Fatan mu shine janyo hankalin gwamnati ta yi abin da ya dace na biyan mu hakokin mu tare da inganta harkar ilimi a kasar wanda shine ginshikin cigaban kasa."

Babu Yajin-aiki, ASUU Sun Jero Matakai 2 da Za Su Dauka a Kan Biyansu Rabin Albashi

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a a Najeriya tana shirin yin zanga-zangar lumuna a fadin Najeriya domin nunawa gwamnatin kasar bacin ranta.

Punch ta rahoto cewa malaman jami’an za suyi zanga-zanga na kwana guda saboda rashin hana su albashi da gwamnatin tarayya tayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel